'Yan bindiga sun shiga tasku: ‘Yan sanda suka fara sintiri ta sama a hanyar Abuja-Kaduna
- Ana ci gaba da kokarin tabbatar da tsaro a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna tare da tabbatar da tsaro ga 'yan Najeriya da ke bin hanyar
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta girke daya daga cikin jiragenta masu saukar ungulu a kan hanyar domin tabbatar da sanya ido ta sararin samaniya
- Sufeto-Janar na ’yan sandan ya je tantance yankin a karshen makon da ya gabata bayan harin 'yan bindiga
Kaduna - Rundunar sintiri ta sama ta rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara aikin sintiri da sa ido a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Matakin dai ci gaba ne da bin umarnin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba na cewa jami’an 'yan sandan Najeriya za su fara tsare hanyar.
IGP da ya ziyarci yankin a karshen makon da ya gabata ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin cewa ‘yan sanda za su tabbatar da tsaro a hanyar tare da tabbatar da tsaro ga duk masu ababen hawa da fasinjojin da ke bin hanyar.
A cewarsa:
"Za mu sauke nauyin da ya rataya a wuyanmu don samun ingantattcen tsaron cikin gida a Najeriya."
Mukaddashin mai magana da yawun hedikwatar rundunar ‘yan sandan, Prince Olumuyiwa Adejobi shi ne ya yada hotunan jigilar jirgin a shafinsa na Twitter.
Zargin hari a Abuja: An baza sojoji a ko'ina saboda su dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin, wani rahoto da jaridar Daily Sun ta fitar na nuni da cewa an jawo hankalin sojojin Najeriya sakamakon rahoton sirri na wani shirin harin ta'addanci da aka shirya kai wa babban birnin tarayya Abuja.
A cewar rahoton, an tura sojoji musamman a kauyuka da kananan hukumomin dake kan hanyar Abuja/Lokoja wato Abaji, Kwali, da Gwagwalada.
Tuni dai wasu daga cikin sojojin suka mika wuya tare da fara gudanar da bincike a yankin Giri da ke kusa da Jami'ar Abuja inda suka sanya shingayen bincike a duk wuraren shiga ko fita cikin birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng