ASUU ga FG: Ba zai yiwu ku yaki rashin tsaro ba yayin da kuka mayar dalibai 'yan zaman kashe wando

ASUU ga FG: Ba zai yiwu ku yaki rashin tsaro ba yayin da kuka mayar dalibai 'yan zaman kashe wando

  • Kungiyar malaman ASUU ta magantu a kan lamarin rashin tsaro da kasar ke fuskanta
  • ASUU ta ce babu yadda za a yi gwamnatin tarayya ta iya yakar rashin tsaro alhalin dalibai na zaune a gida
  • Shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke, ya zargi wasu ministoci da shugaban ma'aikata da bijirewa umurnin Shugaba Buhari na tattaunawa da su domin kawo karshen lamarin

Abuja - Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, sun fadama gwamnatin tarayya cewa ba za ta iya yakar rashin tsaro da ke gudana ba a kasar idan har za ta ci gaba da ajiye dalibai a gida.

Kungiyar ta bukaci yan Najeriya da su daurawa gwamnati alhakin yajin aikinta da ke gudana a yanzu haka, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Allah ya tsarkake mani zuciyata, zan iya mutuwa a gobe, matar tsohon shugaban kasa

ASUU ga FG: Ba zai yiwu ku yaki rashin tsaro ba yayin da kuka mayar dalibai 'yan zaman kashe wando
ASUU ga FG: Ba zai yiwu ku yaki rashin tsaro ba yayin da kuka mayar dalibai 'yan zaman kashe wando Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

ASUU ta kuma yi bayanin cewa ta yi duk mai yiwuwa domin dakatar da lamarin amma abun ya ci tura saboda halin gwamnati na rashin kula da al’amuran da suka kai ga yajin aikin.

Sanarwar ta ASUU na zuwa ne a ranar da Gwamnatin Tarayya ta ce za a sake gwada manhajar UTAS don sanin dacewarta a madadin IPPIS wajen biyansu albashi kamar yadda kungiyar ta bukata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan ya kasance ne duk da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya yi zargin cewa ministocin ilimi, na kwadago da kuma na kudi da shugaban ma’aikatan shugaban kasa sun bijirewa umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na tattaunawa da su domin samar da mafita ga rikicin cikin gaggawa.

Osodeke ya bayyana hakan ne a sakonsa na fatan alkhairi a taron kungiyar likitocin Najeriya.

Da yake magana ta bakin wakilinsa kuma mataimakin shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, Osodeke, wanda ya magantu a taron, ya yi bayanin cewa a yayin ziyarar da Sultan na Sokoto ya kai masa kimanin mako biyar da suka shige, shugaban kasar ya umurci minsitocin da shugaban ma’aikatan da su gaggauta ganawa da ASUU domin samar da mafita kan yajin aikin da ake yi. Ya ce a maimakon haka, sai suka yi biris da shi.

Kara karanta wannan

'Yan siyasan PDP ne suka sankame albashin sojoji a aljifansu, inji gwamnatin Buhari

Ya ce sakataren hukumar jami’o’i na kasa, NUC, ne kadai yake ta halartan ganawarsu tun bayan da aka fara yajin aikin.

Da yake bayyana cewa taken taron kungiyar ta NMA na a kan zukewar kwakwalwa ne, ya ce: “Shine abun da ASUU ke ta fama da shi tsawon shekaru da dama.”

A ruwayar The Sun, Osodeke ya kara da cewa fadan ba wai don jin dadin ‘yan kungiyar ta ASUU ba ne kawai, illa saboda gaba daya tsarin jami’o’in ne wanda har yanzu kimarta ke ci gaba da tabarbarewa.

Shugaban NITDA ya takalo yaki da Malaman Jami’a, ana barazanar karbe masa Digiri

A wani labarin, kungiyar malaman jami’a na reshen jami’ar Abubakar Tafawa Balewa a jihar Bauchi, tana yi wa shugaban NITDA, Kashifu Inuwa, barazana.

Rahoton da ya fito daga jaridar Punch a yammacin Alhamis ya bayyana cewa kungiyar ASUU ta na maganar karbe digirin da aka ba Mal. Kashifu Inuwa.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Ya kara da cewa daliban sun gaji kuma ba za su fasa abin da suka fara ba har zai an bude dukkan jami'o'i a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng