Jami'an 'yan sanda sun ki karbar cin hancin N500k bayan kama mota dankare da miyagun kwayoyi

Jami'an 'yan sanda sun ki karbar cin hancin N500k bayan kama mota dankare da miyagun kwayoyi

  • Jami'an rundunar RRS na jihar Legas sun damke wata bas dankare da miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai miliyan 10
  • Daya daga cikin wadanda aka kama da kwayoyin ya yi yunkurin bai wa 'yan sanda cin hancin N500,000 amma suka ki karba
  • An gano cewa mioyagun kwayoyin mallakin wani Alhaji ne da aka fi sani da Janar a yankin Mushin na jihar Legas

Legas - Jami’an rundunar ta jihar Legas ta tabbatar da cewa ‘yan sandan Najeriya sun kama wata motar bas dauke da miyagun kwayoyi a unguwar Mile 2 da ke jihar Legas.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a Legas, TVC News ta ruwaito.

Jami'an 'yan sanda sun ki karbar cin hancin N500k bayan kama mota dankare da miyagun kwayoyi
Jami'an 'yan sanda sun ki karbar cin hancin N500k bayan kama mota dankare da miyagun kwayoyi. Hoto daga tvcnews.tv
Asali: UGC

Ya ce jami’an rundunar RRS sun damke wata mota kirar bas kuma sun kama wani Ojukwu Omanogho mai shekaru 36 , Hope Jumbo mai shekaru 40 da Oluwole Omojuyitan mai shekaru 40.

Kara karanta wannan

Kaduna: Tashin hankali yayin da mazauna suka tsinci bam a kusa da wani rafi

Hundeyin ya ce a karon farko bincike ya nuna cewa kwayoyin na wani Alhaji ne wanda aka fi sani da Janar a Mushin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kwayoyin na Janar ne, an yi lodin su a cikin wata mota kirar bas da ke Legas mai lamba AGL 205 YD.
“Wani ma’aikacin tawagar masu safarar miyagun kwayoyi ya bayyana cewa sun dauko kayan wanda kudinsa ya kai kimanin Naira miliyan 10 a Alaba Rago da misalin karfe 10 na safiyar ranar Asabar domin jigilarsu zuwa Mushin.
"Duk da haka, dubunsu ta cika a lokacin da jami'an RRS da ke sintiri suka tsayar da bas din a kan binciken da aka saba yi da misalin karfe 4 na ranar Lahadi."

Mista Hundeyin ya ce jami’an sun ki karbar cin hancin N500,000 daga Omojuyitan, dan kungiyar.

“’ Jami'an 'yan sandan sun yi ram da Omojuyitan, wanda da farko ya gudu a kan babur, amma daga bisani ya dawo da N500,000.00 domin bai wa jami’an cin hanci don su sako miyagun kwayoyi da wadanda aka kama kuma ake zargi.

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

Kakakin ya ce, kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Abiodun Alabi, ya jinjinawa kwamandan RRS, CSP Olayinlka Egbeyemi da tawagarsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan ya bayar da umarnin a mika wadanda ak zargi tare da abinda aka kama su da shi zuwa hedkwatar rundunar domin cigaba da bincike.

NDLEA ta kwace wiwi mai nauyin 374.397kg daga masu safara a jihar Kano

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), a jihar Kano ta bayyana yadda ta kama wiwi mai nauyin kilo 374.397, da wasu mutane 131, wadanda ake zargin su da safarar miyagun kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu, 2022.

Kwamandan NDLEA na jihar, Abubakar Idris Ahmad, ya bayyana hakan ne a Kano yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba.

Ya ce, an damko wadanda ake zargin a wurare daban-daban a cikin jihar, bayan tsananta bincike da jami'an rundunar suka yi, inda ya kara da bayyana yadda wadanda ake zargin suka kunshi maza 125 da mata shida.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng