An yi a banza: An kashe N1.3trn amma wutar lantarki bata gyaru ba, ministar kudi
- Ministar kasafin kudi ta Najeriya ta bayyana yadda gwamnatin Najeriya ta kashe kudade da yawa wajen inganta wutar lantarki
- Sai dai, ta koka kan yadda zuba kudaden suka zama kusan aikin banza, domin har yanzu babu wani sauyi a kasar
- Ta bayyana dalla-dalla yadda gwamnati ta shigar da kudi amma ta gagara ganin fa'idar hakan a harkar wutan lantarki
Ministar kasafin kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce kudade Naira tiriliyan 1.3 da gwamnatin tarayya ta tanadar a bangaren samar da wutar lantarki basu haifar da da mai ido ba, inji rahoton TheCable.
A ranar 1 ga Maris, 2017, FG ta amince da kashe N701bn domin inganta wutar lantarki ga Kamfanin Dillalan Wutar Lantarki ta Najeriya (NBET) domin biyan kudin da GenCos ke samarwa ga ma’aikatar wuta ta kasa na tsawon shekaru biyu.
An bayar kudaden ne domin tunkarar kalubalen kudi na wata-wata da GenCos ke fuskanta, yayin da kamfanonin rarraba wuta (DisCos) ke ci gaba da gazawa wajen biyan kudaden wutar lantarkin da ake rarrabawa duk wata.
A cikin wata wasika da ta aike wa shugaban kasa Muhammadu Buhari mai kwanan wata 19 ga watan Nuwamba, 2021, ministar kudi Zainab Ahmed ta yi bayani dalla-dalla yadda za a iya tara kudade ta hanyar sayar da iskar gas don magance kalubalen kudi a fannin.
Kalaman ministar kudi
Ministar ta rubuta cewa:
“Masana’antar na bukatar Naira biliyan 85 a duk wata don biyan kudin iskar gas, samar da wutar lantarki, watsawa da kuma ayyukan rarraba shi.
“Zuba kudade na baya-bayan nan (tsakanin 2017-2019) don magance matsalar wutar lantarki ya hada da na cibiyoyin tabbatar da biyan kudi biliyan 701 da biliyan 600 (PAFs) da aka samu daga Babban Bankin Najeriya (CBN) don kula da wasu lamurra na Gwamnatin Tarayya a bangaren wanda kuma bai haifar da wani gagarumin sakamako ba.
“Tasgaron da aka samu sakamakon babban bambanci tsakanin farashi da kuma abin da ake bukata don daidaita farashi ya jawowa FGN kashe jimillar Naira Biliyan 1.249 tsakanin 2017 zuwa 2019.
“Wadannan kudade an fi bukatarsu wajen bunkasa rayuwar mutane da zuba jarin ababen more rayuwa.
“Ayyukan da ke sama sun hada da wasu ayyuka kamar lamunin Bankin Duniya (har dala biliyan 3) na rage farashi da kuma Euro biliyan 2.6 na shirin samar da wutar lantarki na shugaban kasa duk an yi la’akari da su wajen tallafawa masana’antun samar da wutar lantarki ta Najeriya (NESI).”
Ministar ta kuma bayyana yadda Najeriya ta biya dala miliyan 137 a cikin shekaru biyu na iskar gas da wutar lantarki da ba a taba yin amfani da su ba a yarjejeniyar karba ko biya da kasar ta shiga da wasu masu saka hannun jari a fannin wutar lantarki ba.
'Yan Najeriya miliyan biyu zasu fara karban kudade wata-wata daga Yuni, FG
A wani labarin, gwamnatin tarayya tace zata fara raba wa yan Najeriya Naira Biliyan N20bn daga watan Yuni a tsarin tallafi karkashin shirin National Cash Transfer, kamar yadda Punch ta rahoto.
Bayanai sun nuna cewa FG zata biya yan Najeriya miliyan biyu N5,000 a shirin 'Basic Cash Transfer' da kuma ƙarin N5,000 a tsarin tallafawa talakawa. Jimulla FG zata kashe biliyan N20bn kan mutanen da zasu amfana.
Wani bayani da ya fita a watan Maris, 2022 kan dabaru da kuma tsarin harkokin ma'aikatar jin ƙai da walwalar al'umma ya nuna cewa yan Najeriya dake amfana da shirin ƙara ƙaruwa suke.
Asali: Legit.ng