Nasan za a rina: Limamin masallacin UniAbuja ya yi martani kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid
- Babban limamin masallacin jami'ar Abuja, Farfesa Taofiq Azeez ya yi martani a kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid a matsayin babban limamin masallacin Juma’a na Apo
- Farfesa Azeez ya ce ko daya wannan matakin bai zo masa da mamaki ba domin ya san lallai za a rina
- Sai dai kuma, ya karfafawa Shehin malamin gwiwar ci gaba da aikinsa na alkhairi, cewa kada ya bari hakan ya sanyaya mashi gwiwa
Abuja - Babban limamin masallacin jami'ar Abuja, Farfesa Taofiq Azeez, ya bukaci dakataccen limamin masallacin Apo, Shiekh Nuru Khalid, da kada ya bari gwiwarsa tayi sanyi kan halin da yake ciki a yanzu.
Legit Hausa ta rahoto yadda aka dakatar da Sheikh Khalid bayan wani wa'azi da ya yi a ranar Juma'a.
Da yake magana a ranar Lahadi a taron Ramadana da kungiyar Al-Habibiyyah ta shirya, Farfesa Azeez ya ce dakatarwar da aka yiwa Sheikh Khalid ba abun mamaki bane, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce:
“Hadisin Annabi Muhammadu a kan musanya kuskure da hannu; da harsuna, amma kada ya shiga cikin munanan ayyukan domin ana fifita shi ko girmama shi; sannan su sauya kuskuren da tunaninsu da kuma yi musu addu’a ganin cewa sun canza don shiriya ne ya dace a nan.”
Sai dai kuma, ya bayyana cewa idan shugabanni suka gaza yin abin da ya dace kuma suka kasance masu taurin zuciya, su (malamai) za su iya binciki amfani da zabin Annabi Musa wanda ya nemi fushin Allah a kan shugabanni masu tayar da kayar baya.
Allah Ne Kaɗai Ke Bada Mulki, Kuma Ya Karɓa: Martanin Sheikh Nuru Khalid Bayan Dakatar Da Shi Daga Limanci
Azeez ya ce:
“Na san cewa za su dakatar da shi, kada ya yi kasa a gwiwa, kada ya yi mamaki. Ba mu yi mamaki ba. Ya ci gaba da yin aikin alkhairin. Don haka, sakona zuwa ga Khalid shine cewa kada gwiwarsa ta yi sanyi, kada wannan ya kai shi kasa, ya kamata hakan ya karfafa masa gwiwar kara kaimi.
“Yakamata malamai su shirya ma irin wadannan abubuwan, ana iya dakatar da ku, ana ma iya kai maku farmaki, ana ma iya kashe ku. An kashe shugabanni, masana, malaman addini, annabawa a baya, kada wannan ya sanyayawa kowa gwiwar aikata haka.
“Sai dai kuma, idan kana son yin suka ya zama dole ka kasance da hujjojinka. Kada ka zama mai son kai; dole ku guji nanata zantukan unguwa. Dole ku yi magana kan gaskiya da gaskiya. Ba dole sai kun yi magana kan kiyayya ba, watakila wani ne ya dauki nauyin sa. Wasu lokutan, wasu daga cikin yan siyasan nan na daukar nauyin wasu shugabannin addini don su yi magana kan abokan adawarsu, kada ka kaskantar da kai zuwa ga wannan.”
Ya kuma ga laifin shugabannin addini kan yawancin matsalolin da ke faruwa a kan gazawarsu wajen yin abun da ake tsammani daga garesu, musamman abun da suke wa’azinsu a masallatai da cocina.
Babu hankali a lamarin: Martanin Shehu Sani da wasu 'yan Najeriya kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid
A gefe guda, mun ji cewa an caccaki kwamitin masallacin Abuja bayan dakatar da limamin masallacin Juma'a na Apo Sheikh Nuru Khalid sakamakon caccakar bangarori daban-daban na gwamnati.
Daya daga cikin wadanda suka yi Allah-wadai da matakin dakatar da malamin dai shi ne tsohon dan majalisar dattawa daga Kaduna ta tsakiya kuma mai fafutukar siyasa da zamantakewa, Shehu Sani.
Sani ya bi sahun ‘yan Najeriya da dama don bayyana ra’ayinsa a shafin Twitter. Ya bayyana dakatarwar a matsayin rashin hankali tsagwaronsa.
Asali: Legit.ng