Yan Najeriya miliyan biyu zasu fara karɓan Biliyan N20bn wata-wata daga Yuni, FG
- Gwamnatin tarayya tace zuwa watan Yuni zata fara biyan talakawan Najeriya miliyan biyu makudan kuɗi duk wata
- Gwamnatin tace kowane mutum ɗaya daga cikin waɗan da zasu ci gajiyar shirin zai karbi N5,000 da ƙarin wasu N5,000 na daban
- A jumulla, gwamnati zata kashe Naira Biliyan N20bn duk wata kan mutum miliyan biyu
Abuja - Gwamnatin tarayya tace zata fara raba wa yan Najeriya Naira Biliyan N20bn daga watan Yuni a tsarin tallafi karkashin shirin National Cash Transfer, kamar yadda Punch ta rahoto.
Bayanai sun nuna cewa FG zata biya yan Najeriya miliyan biyu N5,000 a shirin 'Basic Cash Transfer' da kuma ƙarin N5,000 a tsarin tallafawa talakawa. Jimulla FG zata kashe biliyan N20bn kan mutanen da zasu amfana.
Wani bayani da ya fita a watan Maris, 2022 kan dabaru da kuma tsarin harkokin ma'aikatar jin ƙai da walwalar al'umma ya nuna cewa yan Najeriya dake amfana da shirin ƙara ƙaruwa suke.
Rahoton ya bayyana cewa a 2018, tsarin tallafin ya mamaye jihohi 18, daga bisani ya ƙara faɗaɗa zuwa jihohi 24 a 2019, kuma ya ƙarisa shiga baki ɗaya jihohi 36 da Abuja a 2022, ya haɗa mutum miliyan 1.6m.
Amma ministar jin ƙai da walwalar al'umma, Sadiya Umar Farouƙ, ta bayyana cewa adadin mutanen da zasu amfana da shirin zuwa watan Yuni zai ƙaru.
A karkashin shirin gwamnatin tarayyya na tallafawa talakawa da magidanta masu ƙaramin karfi duƙ wata.
Sadiya Farouk ta ce:
"Zuwa watan Yuni, 2022 zamu fara biyan mutum miliyan biyu N5,000 da ƙarin N5 000 na Conditional Cash Transfer wanda zasu taimaka musu wajen kula da lafiya, biyan kuɗin makaranta da gyara muhallen su."
Ministan ta kuma yi bayanin cewa ma'aikatarta ta kirkiri tsarin RRR Wanda ke ɗauko bayanan talakawan dake rayuwa a karkara musamman waɗan da kullen korona ya shafe su da hanyar kudin shigar su.
"Zuwa yau, mutum miliyan ɗaya da gwamnati ta nufa, mun biya N5,000 ga mutum 850,000 ta hanyar amfani da fasahar zamani wajen tura kuɗi, kuma sai da aka tantace kowane asusu kafin angiza kuɗin."
"Zuwa ƙarshen watan Afrilu, za mu biya ragowar mutum 150,000. Kuma kowane mai cin gajiyar shirin zai samu kuɗin tallafi na tsawon wata shida.
Tsarin N-Power?
Ma'aikatar jin ƙai da walwala ta ƙara da cewa tsarin shirin N-Power ya samar da aikin wucin gadi ga matasan da suka kammala karatu 498,602 a rukunin A da B, yayin da yanzu haka aka ɗauki mutum 450,000 a rukunin C-1.
Ta kara bayanin cewa yanzu haka akwai wasu 390,000 da aka fara shirin ɗauka a Rukunin C-2, duk a ƙarƙashin umarnin shugaban ƙasa na kara ɗaukar mutum miliyan ɗaya.
A wani labarin kuma Babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Gombe ya sauya sheka zuwa APC mai mulki
Tsohon hadimin tsohon gwamnan jihar Gombe, Barista Abdulƙadir Yahaya, ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC mai mulki
Tsohon mashawarci kan harkokin siyasa ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda ɗumbin ayyukan cigaba da gwamna ke yi.
Asali: Legit.ng