Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane har da ɗan Kwamishinan jiha
- Jim kaɗan da gama Sallan dare ta watan Azumi yan bindiga suka buɗe wa mutane wuta a garin Tsafe dake jihar Zamfara
- Mazauna yankin sun tabbatar da cewa yan ta'addan sun halaka mutane da dama ciki har da ɗan kwamishinan harkokin tsaro na jiha
- Har yanzun hukumomin Zamfara ba su ce komai ba game da harin, mutane sun fara guduwa daga garin
Zamfara - Wasu yan bindiga ranar Lahadi da daddare, sun kai hari garin Tsafe, hedkwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, sun halaka mutane da dama.
Mazauna garin sun bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗan da aka kashe shi ne ɗan Kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Mamman Tsafe.
Sai dai har yanzun, kwamishinan da kuma gwamnatin Zamfara ba su ce uffan ba dan tabbatar da lamarin a hukumance.
Haka nan, kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, bai ɗaga kiran wayan da Premium Times ta masa ba, kuma be turo amsar sakonni ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mazauna garin sun bayyana cewa yan bindigan sun shigo garin jim kaɗan da gama Sallan Tarawihi, suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.
Wani mazauni ya faɗa wa Daily Trust cewa:
"Yan ta'addan sun farmaki yankin Shiyar Namada wanda ke kusa da gidan kwamishinan sanye da kayan sojoji, da mutane suka gan su, sun ɗauka jami'an tsaro ne suka zo Sintiri, shiyasa ba su ankarar da mutane ba."
"Ɗan kwamishinan tare da wasu mutane na zaune a kofar gidan mahaifinsa lokacin buɗe baki, yayin da maharan suka shigo, suka buɗe wuta kan duk wanda suka gani."
Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan sun halaka aƙalla mutum uku, kuma lamarin ya auku a yankin Hayin Tumbi kusa da gidan Kwamishinan, yayin da wasu ke cikin Masallaci ba su gama Sallah ba.
Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari kauyuka huɗu da tsakar rana a Zamfara, rayuka sun salwanta
Bayan harin, mutane da yawa sun tattara kayansu sun bar garin domin tseratar da rayuwarsu.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda, Muhammad Shehu, bai ɗaga kiran waya ba yayin da aka tuntuɓe shi domin yin tsokaci da daren ranar Lahadi.
Sai dai wata majiya daga cikin rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin da kuma kashe ɗan kwamishinan harkokin tsaro.
Majiyar ta ƙara da cewa akwai yuwuwar hukumar yan sanda ta fitar da sanarwa a hukumance game da sabon harin da safiyar Litinin (yau).
Harin na jiya Lahadi da daddare shi ne na baya-bayan nan da yan bindiga suka kai, waɗan da suka kwashe shekaru suna aikata ta'addanci a jihar da maƙotanta.
Yan ta'addan sun cigaba da kai hari duk da umarnin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na kawo ƙarshen su da kuma ƙara jibge jami'an tsaro a yankunan.
A wani labarin kuma Shugaban matasan APC da wani babban jigo sun yi hatsari, Allah ya musu rasuwa
Allah ya yi wa shugaban matasan APC rasuwa da wani mamba da suke tare sanadiyyar hatsarin Mota a jihar Oyo.
Rahoto ya nuna cewa mutanen biyu na cikin Mota a kan hanyarsu ta komawa gida wata Tirela ta dakon siminti ta niƙe su.
Asali: Legit.ng