Wadanda suka sace basaraken Abuja sun nemi iyalansa su siyar da gidansa don hada masu miliyan N20 kudin fansa
- Yan bindigar da suka sace basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali ta birnin tarayya sun nemi a saka gidansa a kasuwa domin hada masu naira miliyan 20
- Sun sha alwashin ci gaba da rike shi har sai an hada kudin koda kuwa zai shekara a hannusu ne
- Sai dai kuma, yan uwansa sun ce gidan da yake zaune a ciki ko naira miliyan 5 ba sai kai ba
Abuja - Wadanda suka yi garkuwa da basaraken garin Bukpe da ke yankin Kwali ta birnin tarayya sun umurci iyalansa da su siyar da gidansa domin hada naira miliyan 20 da suka bukata na fansarsa.
Daily Trust ta rahoto yadda masu garkuwa da mutane suka farmaki fadar basaraken, Mai Martaba Alhaji Hassan Shamidozhi, a daren ranar Laraba.
Jaridar ta kuma rahoto cewa a lokacin da ta ziyarci garin a ranar Lahadi, wani ahlin gidan basaraken, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce masu garkuwa da mutanen sun sha alwashin cewa ba za su sake shi ba har sai sun samu naira miliyan 20.
Ya ce:
“A zahirin gaskiya, har a safiyar Asabar, sun kira sannan suka umurci ahlin da su je su siyar da gidansa domin su iya hada masu naira miliyan 20 na fansarsa.
“Daya daga cikin ahlin da suke tattaunawa da su ya fada masu cewa hatta gidan da jagoran ke zama bai kai naira miliyan 5 ba.”
A cewarsa, shugaban masu garkuwa da mutanen yay i barazanar tsare basaraken a hannunsu koda kuwa zai kai su tsawon shekara ne don hada naira miliyan 20 na fansarsa.
Ahlin gidan Ahmed Joel, wani mazaunin yankin da aka yi garkuwa da shi tare da diyarsa Precious ya bayyana cewa masu garkuwan sun nemi naira miliyan uku kudin fansa.
Zuwa yanzu ba a ji ta bakin kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ba game da bukatar biyan fansar.
Yan bindiga sun kutsa fadar babban Basarake a Abuja, sun sace shi
A baya mun ji cewa Sarkin gargajiya na yankin Bukpe, yankin ƙaramar hukumar Kwali a birnin Abuja, Mai Martaba (HRH) Alhaji Hassan Shamidozhi, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.
Ɗan uwan Basaraken, wanda shi ne babban Limamin babban Masallacin yankin, Malam Jibrin D. Gimba, shi ya tabbatar da haka ga jaridar Dailytrust.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru da ɗan uwansa da misalin ƙarfe 9:32 na daren ranar Laraba, 30 ga watan Maris, 2022.
Asali: Legit.ng