Malaman Addini Sun Buƙaci Buhari Ya Bada Umurnin a Fara Yi Wa Ƴan Bindiga Ruwan Bama-Bamai a Dazuka
- Wata kungiya ta malaman addinin mai suna 'Pastors United for Change Association' ta yi kira ga FG ta fara kaiwa yan bindiga hari a mabuyarsu
- Kungiyar ta bakin jagoranta ta roki Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da matsayinsa ya bada umurnin a yi amfani da jirgin yakin Super Tucano a yi wa yan bindiga ruwan wuta
- Kungiyar ta kuma roki yan Najeriya su yi amfani da falalar watan Ramadana su yi addu'o'in Allah ya bamu zaman lafiya a Najeriya ya shiga tsakaninmu da miyagu
Wata kungiyar shugabannin addini a karkashin 'Pastors United for Change Association' ta yi kira ga gwamnatin tarayya da sojoji sun fara kaddamar da babban hari da ruwan bama-bamai a mabuyar yan bindiga a arewa maso yamma da jihar Niger, rahoton Channels TV.
Shugabannin addinin kuma sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da matsayinsa na shugaban hafsoshin tsaro ya bada umurni a yi amfani da sabbin jiragen yaki na Super Tucano a yi wa bindiga ruwan wuta a daji kamar yadda Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya bada shawara.
Sun kuma yaba da gwamnan na Jihar Kaduna bisa matakan da ya ke dauka na tabbatar da ganin an samu zaman lafiya a jihar kamar yadda Channels TV ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da ya ke jawabi wurin taron manema labarai a Kaduna, Shugaban United Pastors for Change, Apostle David Adeniran, ya koka kan yadda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon harin yan bindiga a Kaduna da wasu jihohin yana mai cewa abin ya fi karfin gwamnoni.
Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su kara zage damtse domin ganin an kamo wadanda ke kashe-kashe da kai hari an kuma hukunta su.
Harin Jirgin Ƙasa: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai
A bangarensa, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya lashi takobin yin hayar sojoji daga kasashen ketare don su taya yaki da ‘yan ta’adda bayan harin da suka kai wa jirgin kasa a Kaduna ranar Litinin.
Ya kuma lissafo jihohi 4 na yankin arewa maso yamma, inda ya ce akwai yuwuwar su bi sahun shi. Jihohin sun hada da Zamfara, Kebbi, Katsina da Sokoto, The Punch ta ruwaito.
Ya ce zasu dauki wannan matakin ne matsawar gwamnatin tarayya bata dauki wani matakin a zo a gani ba a yankin.
Asali: Legit.ng