Rago Ne, Tserewa Ya Yi Daga Filin Daga: Martanin Rundunar Soja Kan Bidiyon Neman Taimako Da Wani Soja Ya Fitar

Rago Ne, Tserewa Ya Yi Daga Filin Daga: Martanin Rundunar Soja Kan Bidiyon Neman Taimako Da Wani Soja Ya Fitar

  • Rundunar sojojin Najeriya, ta yi tsokaci game da bidiyon da wani soja ya fitar inda ya ke rokon a kai masa taimako
  • Rundunar sojojin ta ce binciken da ta fara yi a halin yanzu ya nuna cewa sojan ya tsere ne daga filin daga a Gurara Jihar Niger, ya yi bidiyon don boye ragwancinsa
  • Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojojin ya kara da cewa abin da sojan ya aikata ya saba wa ka'idar aikin rundunar sojan Najeriya

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta yi magana game da bidiyon sojan nan da ya bazu a shafukan sada zumunta inda ya ke neman taimako, yana ikirarin yan uwansa sun tafi sun bar shi.

Gidan sojan ta ce abin da sojan ya aikata ba komai bane illa neman boye ragwancinsa amma ba watsi da shi aka yi ba, kamar yadda The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Na kaɗu da kashe-kashen dake faruwa a kusa da birnin Abuja, Kwankwaso ya yi magana

Rago Ne, Tserewa Ya Yi Daga Filin Daga: Martanin Rundunar Soja Kan Bidiyon Neman Taimako Da Wani Soja Ya Fitar
Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Tsere wa sojan ya yi daga filin daga, Onyema Nwachukwu

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar soja, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce binciken da aka yi na nuna sojan ne ya tsere ya bar abokan aikinsa yayin wani aiki da suka tafi yi a Gurara, Jihar Niger.

Abin da sojan ya aikata ya saba wa dokokin Rundunar sojan Najeriya, Onyema Nwachukwu

A cewarsa, abin da sojan ya aikata ya saba wa dokar aikin Rundunar Sojojin Najeriya, ya kara da cewa sojan ya aikata hakan ne don kawar da hankalin mutane daga ragwancinsa.

Sanarwar ta ce:

"Akasin ikirari da abin da sojan ke neman nuna wa a bidiyon, binciken da aka fara yi sun nuna cewa bidiyon wani yunkuri ne da gangan na kare kansa daga zargin ragwanci, bayan ya gudu ya bar abokan aikinsa yayin wani hari da suka kai a Gurara, Jihar Niger."

Kara karanta wannan

Minista ya saba alkawari, ya ce aikin Ajaokuta da ake jira tun 1979 ba zai kammalu a 2023 ba

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

A wani labarin, kun ji cewa wani Akeem Ogunnubi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola cikin ranakun karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode dama ya bayar da labari yayin tasa keyar mutumin da ake zargi cewa wasu maza dauke da bindigogi sun sace wani dan canji har cikin ofishinsa a ranar 30 ga watan Disamban 2021 da misalin karfe 5:30 da yamma.

Wanda lamarin ya faru da shi kamar yadda Olukode ya shaida ya ce sun zarce da shi daji ne sannan suka bukaci kudin fansa kafin su sake shi, a nan su ka yi masa kwacen N204,000 sannan suka tsere suka bar shi a wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164