Labari mai dadi: Kotu ta hana DSTV da GoTV kara wa 'yan Najeriya kudin 'subscription'
- Kotu ta bukaci MultiChoice Nigeria Limited da kar ya kara farashin kayayyakinsa da ayyukansa a Najeriya
- Kotun kayayyaki ta Competition and Consumer Protection (CCP) ne ta bayar da umarnin hana kamfanin kara farashi a Abuja
- Kotun ta bayar da wannan umarni ne biyo bayan wata kara da wani lauya Festus Onifade ya gabatar a gabanta
Wata kotu da ke zamanta a Abuja, mai suna Competition and Consumer Protection (CCP) ta haramtawa Kamfanin Multichoice Nigeria Limited kara farashin kayayyakinsa da ya kudurta daga ranar 1 ga Afrilu, PM News ta ruwaito.
Kotun mai mambobi uku a karkashin jagorancin Thomas Okosun, ta bayar da wannan umarni ne biyo bayan wata karar da lauya Festus Onifade ya gabatar a madadin sa da kuma kungiyar hadin kan masu amfani da kayayyaki a Najeriya.
Sauran mambobin kotun sun hada da Sola Salako Ajulo da Ibrahim EL-Yakubu., kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito.
NAN ta ruwaito cewa a cikin karar mai lamba: CCPT/OP/1/2022, Multi-Choice Nigeria Limited da Federal Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC) sune masu amsa karar na 1 da 2.
An gabatar da karar ne a ranar 29 ga Maris bisa ga sashe na 39 (1) & (2) na dokar FCCPC 2018; oda 26, Doka ta 5 (2), (3) & 26 Doka ta 6 (1) & (2) Dokokin Babban Kotun Tarayya (Tsarin Farar Hula) Dokokin 2019 da Sashe na 47 (a), (b), (c), (d) , na Federal Competition and Consumer Protection 2018.
Karar dai ta nemi dakile kamfanin na MultiChoice daga shirinsa na kara farashi, wanda ya koka da cewa farashin man fetur ya karu a Najeriua.
Kotu ta yi duba, sannan ta ba da umarnin kada kamfanin ya aikwatar da manufarsa ta karin kudin farashin.
Tsadar rayuwa: DSTv, GOTv za su kara kudin 'subscription' yayin da Ramadana ke karatowa
A tun farko, wani rahoton jaridar Punch ya nuna alamar cewa, masu amfani da DSTv da GoTV a Najeriya za su fara biyan sabon farashi don kallon shirye-shirye a tashoshin da suka fi so, Multichoice ya sanar.
Sabon farashin wanda aka sanar wa jama'a a yau, Maris 22, 2022, kamfanin ya ce ya faru ne saboda hauhawar farashin kayayyaki da dawainiyar kasuwanci.
Sabbin sauye-sauyen za su fara aiki ne daga Afrilu 1, kuma zai shafi dukkan tsarukan hulda na nau'ikan kamfanin guda biyu, rahoton PremuimTimes.
Asali: Legit.ng