Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

  • Wani labari mara dadi da ke iso mu ya bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun farmaki wani yankin Zamfara
  • Harin ya kai ga hallaka wani basarake a jihar, tare da yin garkuwa da wasu mutane bayan hallaka da dama
  • Shugaban karamar hukuma a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, amma 'yan sanda basu ce komai akai ba

Zamfara - Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata sun kai hari a wasu kauyuka a kananan hukumomin Talata Mafara da Bakura a jihar Zamfara inda suka kashe mutane da dama.

Premium Times ta tattaro cewa al’ummar da abin ya shafa sun hada da Ruwan Gora da Ruwan Gizo (a Talata Mafara) da ‘Yar geda (a Bakura).

Harin 'yan bindiga a jigar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Majiyoyin yankin sun shaida wa jaridar cewa ‘yan bindigar sun kashe hakimin kauyen Yargeda, Abdu Umaru.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka jama'a masu yawa a sabon harin da suka kai Benue

Kabiru Muhammad, wani ma’aikacin gwamnati kuma mazaunin garin Bakura, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun isa yankin ne da misalin karfe 11:45 na rana.

Gaskiyar abinda ya faru, daga bakin wani mazaunin yankin

A cewarsa:

“Kamar yadda suka saba, sun zo ne a kan babura suka fara harbe-harbe ba kakkautawa a lokacin da suka shiga kauyen. Kana iya jin karar harbe-harbe daga babban garin Talata Mafara. Bayan harin, an kashe mutane hudu ciki har da hakimin kauyen, wanda aka kashe a cikin gidansa.
"An kashe wasu a cikin al'umma. An yi garkuwa da wani dan kasuwa mai suna Malami Shehu da wasu mutane da dama."

Muhammad, ya ce ba za su iya tantance adadin wadanda aka kashe ba, domin a cewarsa, wasu mazauna yankin sun shiga daji yayin harin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun kashe 9 a jihar Neja

Shugaban karamar hukuma ya tabbatar da faruwar lamarin

Shugaban karamar hukumar Talata Mafara, Dahiru Maiyara, ya tabbatar da harin da aka kai wa al’ummar.

Ya kuma tabbatar da cewa mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, kwamishinan ‘yan sanda, Ayuba Elkana da sauran su sun ziyarci al’ummomin da aka kai wa harin.

Shi ma dan majalisar wakilai mai wakiltar Anka/Talata Mafara, Kabiru Yahaya, ya yi Allah-wadai da hare-haren, inda ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ta kare al’ummarta.

Har yanzu dai hukumomin ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

'Yan bindiga sun sace jami'in kwastam, dansa da wasu mutum 8 a sabuwar harin da suka kai a Kaduna

A labari makamancin wannan, an sace wani jami'in kwastam mai suna Gambo Turaki da wasu mutane tara a Kofar Gayan Low-Cost Zaria a Jihar Kaduna.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan sun afka wurin ne misalin karfe 9 na daren ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ba a gama jimamin harin jirgin kasa ba, 'yan bindiga sun hallaka mutum 23 a Kaduna

Wannan shine karo na biyu da yan bindiga ke kai hari Kofan Gayan Low Cost suna sace mutane.

A bara, yan bindiga sun kutsa unguwar sun sace matar wani jami'in kwastam da wata mata, sun sako su bayan an biya fansar N15m.

A wani labarin na daban, akalla masu laifi biyar ne suka tsere daga ofishin yan sanda dake yankin Awak dake karamar hukumar Kaltango a jihar Gombe.

Uku daga cikin wanda ake zargin an kama su, amma sauran biyu ana neman su har yanzu a lokacin hada wannan rahoton, kamar yadda The punch ta ruwaito.

Wannan na kunshe cikin wani jawabin manema labarai wanda mai magana da yawun hukumar yan sanda, Mahdi Abubakar ya sanyawa hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.