Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa fadar babban Basarake a Abuja, sun sace shi
- Masu garkuwa sun shiga har cikin fada sun yi awon gaba da wani babban Basarake a birnin tarayya Abuja
- Ɗan uwan Sarkin, wanda yake limami a yankin, Malam Gimba, ya ce lamarin ya faru da daren ranar Laraba
- Yace sai bayan awanni da faruwar lamarin wasu yan sanda suka ƙariso, kuma ba su jima ba suka yi gaba abin su
Abuja - Sarkin gargajiya na yankin Bukpe, yankin ƙaramar hukumar Kwali a birnin Abuja, Mai Martaba (HRH) Alhaji Hassan Shamidozhi, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.
Ɗan uwan Basaraken, wanda shi ne babban Limamin babban Masallacin yankin, Malam Jibrin D. Gimba, shi ya tabbatar da haka ga jaridar Dailytrust.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru da ɗan uwansa da misalin ƙarfe 9:32 na daren ranar Laraba, 30 ga watan Maris, 2022.
Ya ce Basaraken, wanda ya fito gaban fadarsa domin shan iska, an yi awon gaba da shi bayan nuna masa bindiga.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Channesl tv ta rahoto Limamin ya ce:
"Ban jima da komawa gida ba daga fadarsa bayan ya faɗa mun zai yi wanka daga nan ya fito kofar fadarsa ya sha iska. Mintuna kaɗan sai na fara jin ƙarar harbe-harben bindiga."
"Lokacin da na leƙa ta tagar ɗakina sai na hangi masu garkuwan sun yi awon gaba da shi."
Ko maharan sun kira domin neman kuɗin fansa?
Gimba ya bayyana cewa har yanzun yan ta'addan ba su tuntubi kowa ba kuma wannan lamarin shi ne karo na uku da ya faru a yankin su.
Yace awannin bayan sace Sarkin, wasu jami'an yan sanda suka shigo yankin. amma bayan wani ɗan lokaci suka kama gabansu.
Duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin hukumar yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, ya ci tura domin ba ta ɗaga waya har yazun.
Har zuwa yau Alhamis da safe, Mutane na cigaba da tururuwan zuwa jaje fadar mai martaba Sarkin da aka sace.
A wani labarin kuma Shugaban matasan APC da wani babban jigo sun yi hatsari, Allah ya musu rasuwa
Shugaban matasan APC na ƙaramar hukumar Ogbomoso North a jihar Oyo, Afolabi Tunde, da wani mamba mai suna Sabitu, sun yi hatsari a yankin Ogbomoso.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata Tirela ta dakom Siminti ce ta bugi motarsu shugaban matasa a tashar Caretaker bus stop, Ogbomoso.
Asali: Legit.ng