Kaduna Ta Kudu: An Sanya Wa Shanu 21 Guba Duk Sun Ci Sun Mutu a Karamar Hukumar Jema'a
- A ranar Juma’a da yamma shanu 21 suka mutu bayan sun shan guba a Gidan Waya da ke karkashin karamar hukumar Jema’a a Jihar Kaduna
- Kakakin Kungiyar Makiyayan Shanu ta Miyetti Allah, reshen Jihar Kaduna, Ibrahim Bayero ya ce shanun mutane 3 ne, Pate Gambo, Iliyasa Gambo da Inuwa Gambo
- Shugaban karamar hukumar Jema’a, Kwamared Yunana Markus Barde ya shirya taro don kawo hadin kan manoma da makiyayan Gidan Waya
Kaduna - Shanu 21 sun mutu a ranar Juma’a da yamma inda ake zargin guba aka sanya musu a kusa da kwalejin ilimin Jihar Kaduna (KSCOE) ta Gidan Waya da ke karamar hukumar Jema’a, Jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.
Yayin tattaunawa da Daily Trust dangane da lamarin, kakakin kungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah, reshen Jihar Kaduna, Ibrahim Bayero ya ce shanu guda 15 na Pate Gambo ne, 5 na Iliyas Gambo sai kuma daya na Inuwa Gambo ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Don kwantar da tarzoma, shugaban karamar hukumar Jema’a, Kwamared Yunana Markus Barde ya shirya taro don kawo hadin kan manoma da makiyayan Gidan Waya da ke karkashin masarautar Godogodo da kuma makwabtansu ‘yan Fulani akan kisan shanu wadanda ake zargin guba aka basu.
Shugaban karamar hukumar Jema’a ya nuna rashin jin dadinsa akan lamarin
Yayin bayani dangane da taron, shugaban karamar hukumar ya nuna rashin jin dadinsa inda ya ce manoma ne suka shirya wannan tuggun don tayar da tarzoma.
Kwamared Barde ya tausaya wa wadanda shanunsu suka mutu kuma ya tabbatar da cewa zai sanar da hukuma kuma ya nemi gwamnati ta dauki mataki akai.
Ya ja kunnen jama’a akan yin abubuwan da zasu tayar da hankula kuma ya ce duk wanda aka kama zai fuskanci fushin hukuma.
Yayin tattaunawa da hakimin Godogodo, Dr Habila Saidu, ya yaba wa Fulanin Gidan Waya, musamman wadanda aka halaka wa shanu, inda ya ce sun bi doka.
Wani Malam Ahmadu ya ce wadanda aka halaka wa shanu sun amshi kaddararsu
A bangaren Mallam Gambo Ahmadu, wanda ya yi jawabi a maimakon wadanda aka halaka wa shanu, ya ce shugabannin yankin sun tausaya musu tare da basu baki wanda hakan ya ja suka amince da kaddarar su.
Ya kuma nemi taimakon gwamnati akan ta kawo dauki ga wadanda suka tafka asarar.
Taron ya samu halartar manyan mutanen yankin ciki har da DPO na karamar hukumar Jema’a, Dantsoho Lau Abdullaho, OC, DSS Ibrahim Habu da kuma wakilin kwamandan Sector Seven na Operation Save Heaven, Colonel Timothy Opurum da sauransu.
Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250
A wan labarin, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.
Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.
Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.
Asali: Legit.ng