Shugaban UN yayi Allah wadai da harin jirgin kasan Abuja-Kaduna
- Shugaban majalisar dinkin duniya ya bayyana takaicinsa game da harin da aka kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna
- Yayi kira ga hukumomin tsaro dasu duk mai yiyuwa wajen damke tsagerun yan ta'addan
- Ya kuma yi Allah wadai da harin da wasu yan bindigan suka kai filin jirgin saman Kaduna ranar Asabar
Shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres yayi Allah wadai da harin da wasu tsagerun yan bindiga suka kai jirgin Abuja-Kaduna, wanda ya haddasa mutuwar mutane da yawa wasu suka jikkata sannan aka yi garkuwa da wasu.
Guterres a wani jawabi jiya, ya tura sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, ya kuma yi fatan samun lafiya ga wadanda suka jigata sannan yayi addu'ar kubutar da wadanda ke hannun miyagun.
Shugaban ya yi kira ga hukumomin tsaro da su zage damtse wajen kamo duk wadanda suke da hannu a wannan ta'addancin.
Ya kara jaddada taimako da goyan bayan majalisar dinkin duniya ga gwamnati da mutanen Nijeria a yakin da suke yi da ta'addanci, cin zarafi da wasu laifuffuka.
Bayan haka ya kuma yi Allah wadai da harin da miyagu suka kai filin jirgin saman Kaduna ranar Asabar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Mr Samuel Aruwan, ne ya tabbatar da harin a wani jawabi ranar Asabar.
Aruwan yace dakarun dake ciki da wajen filin ne suka tunkari tare da kore yan bindigan.
Har ila yau, yan bindigan sun harbe tare da kashe wani ma'aikaci wanda ya fara hangensu kuma ya sanar.
Gwamnatin jihar Kaduna ta saki takardar jerin sunayen fasinja
A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Kaduna ta saki takardar jerin sunayen fasinja na jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna mai suna AK9 wanda wasu ‘yan bindiga suka kai wa hari a daren ranar Litinin, 28 ga watan Maris.
Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
A cewar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na jihar Kaduna a wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, 30 ga watan Maris, ya ce takardar ta nuna cewa fasinjoji 398 ne suka sayi tikitin tafiya amma 362 daga cikin wadannan fasinjoji suka shiga jirgin.
Wannan lamari ya tada hankalin jama'a saboda dangi da dama sun bayyana damuwa kasancewar basu ji labarin halin da 'yan uwansu ke ciki ba har zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng