Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Tinubu Ya Nemi a Tara Wa Iyalan Waɗanda Suka Jikkata Kuɗi
- Bola Tinubu ya yi kira ga jama’an Najeriya akan hada kudade ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka ji raunuka a harin jirgin kasan Kaduna
- Dama tun kafin nan Tinubu ya dakatar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa washegarin da aka kai harin a jihar ta arewa maso yammacin kasar nan
- Tsohon gwamnan Jihar Legas din ya kwatanta harin a matsayin makurar zalunci yayin da ya yi kira ga hukumomin tsaron Najeriya akan kawo karshen matsalolin tsaron kasar nan
Legas - Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ‘yan Najeriya akan hada kudade ga fasinjojin jirgin kasan da suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka raunana sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai Kaduna a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.
Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas ya yi wannan kiran ne ta wata takarda wacce Legit.ng ta gani a ranar 29 ga watan Maris.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamensa:
“Mu ‘yan uwan juna ne. Wajibi ne mu taimaka wa ‘yan uwanmu maza da mata a wannan lokacin. Ya kamata mu yi kokarin kwantar wa wadanda hari ya sama a lokacin nan na tsanani don kara kawo hadin kai da dunkulewar juna.”
Tinubu ya ce wajibi ne jami’an tsaro su kawo karshen harin da ‘yan bindiga suke kaiwa bangarorin kasar nan.
Tinubu ya yi addu’a ga wadanda suka raunana ko suka rasa rayukansu
Ya kula da cewa:
“Ya zama dole mu kawo karshen wadannan masifun da ke damun bangarori daban-daban na kasar nan. Ba za mu tsaya ba har sai mun kawo zama lafiya a kasar nan.
“Ina mai nuna alhinina da bakin ciki tare da mika addu’o’ina ga wadanda suka raunana. Ina fatan su warke. Kuma da yardar Ubangiji sai an yi musu adalci ta hanyar kawo wadanda suka cutar da su gaban shari’a.”
Harin Jirgin Kasa: Shugaban Kungiyar Yan Kasuwan Najeriya Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe
A bangare guda, Mambobin kungiyar ‘Yan kasuwan Najeriya, TUC, suna cikin wadanda harin da aka kai jirgin kasa ranar Litinin a Jihar Kaduna ya ritsa da su har suka rasa rayukansu.
Daily Trust ta tattaro yadda babban sakataren kungiyar TUC na kasa, Barista Musa-Lawal Ozigi da shugaban kungiyar na Jihar Kwara, Kwamared Akinsola Akinwunmi suka halaka sakamakon harin.
Wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin jin dadinsu dangane da harin.
Asali: Legit.ng