Hanyoyi 5 na musamman da Musulmi zai bi ya shirya zuwa watan Ramadan Mai Albarka

Hanyoyi 5 na musamman da Musulmi zai bi ya shirya zuwa watan Ramadan Mai Albarka

  • Yayin da watan Azumin Ramadana ke kara gabatowa, akwai bukatar kowane Musulmi ya shirya domin ribatar watan mai Alfarma
  • Mun tattara muku wasu hanyoyi 5 da zasu taimaka wajen shirya zuwan watan wanda yake wajibi da baligi ya azumci watan
  • Shirya manufa na ɗaya daga cikin abubuwan da ake bukata kowane Musulmi ya yi domin shiga Inuwar Allah a watan

Watan Ramadan, wanda shi ne wata na Tara a jerin watannin Musulunci, lokaci ne mai Albarka da babu kamarsa ga Al'ummar Musulmi a faɗin duniya.

Azumtar wannan wata na ɗaya daga cikin shika-shikan Addinin Musulunci kuma wajibi ne ga kowane Musulmi da ya kai matakin Balaga ya yi Azumin kwana 29 ko 30.

Ramadan na fara wa ne daga lokacin da shugabannin Musulmai suka sanar da ganin jinjirin wata a kowace ƙasa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari

Hanyoyin shirya zuwan watan Ramadana.
Hanyoyi 5 na musamman da Musulmi zai bi ya shirya zuwa watan Ramadan Mai Albarka Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shiga Ramadana na bukatar shiri na musamman ga duk wani mai Imani domin yin Azumi kamar yadda Allah SWT ya ba da umarni kuma Manzon Allah (SAW) ya koyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta tattara muku wasu hanyoyi biyar na musamman da Zaku shirya zuwan Ramadan wanda ka iya farawa ranar Lahadi.

Duba lafiya

Zama cikin ƙoashin lafiya babban jigo ne da ake bukata ga mai Azumi domin duk wanda ba shi da lafiya kuma zata iya jefa shi cikin hatsari idan ya ɗau Azumi, an umarci ya aje.

Zuwa duba lafiya kafin zuwan watan Ramadana na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin shiryawa tsawon wata ɗaya na Azumin wajibi, musamman idan mutum ya ji alamun ba shi da lafiya.

Yana da kyau Musulmi ya tabbatar da lafiyarsa kafin fara Azumi ko kuma ya yaƙi rashin lafiyar dake damunsa wacce ka iya hana shi yin Ibada cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

Saita Manufofin da kake son cimma a Ramadan

Kasancewar watan Azumin Ramadan ya kasu kashi uku; Rahama, Gafara da kuma yanta bayi daga wuta, kowane Musulmi na da bukatar ya kudiri manufofin da zai cimma wa a watan domin samun Rabo.

Wannan zai haɗa da, Sadaƙa, Ciyar da mabuƙata, Addu'a da kuma karanta Littafi mai tsarki Alƙur'ani. Zama da jera irin waɗan nan manufofi zai taimaka.

Kula da cin abinci

A lokacin watan Ramadan, Musulmai na kamewa daga ci ko sha, ko saduwa da iyali tun daga fitowar rana har zuwa faɗuwarta. Saboda haks kana bukatar ƙarfi da kuma gina jikinka.

Bayan haka, Musulmi na bukatar a kowace rana ya kula da cin abincinsa ya bai wa kowane kalar abincin da jiki ke bukata haƙƙinsa kafin da kuma bayan buɗa baki.

Kana bukatar cin abinci mai gina jini, abincin da aka noma daga ƙasa, Bitamin da kuma shan ruwa sosai da sauran kashe-kashen abinci da jiki ke bukata.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Tsagin hamayya na kulla-kullan ruguza Najeriya' Gwamnatin Buhari ta fallasa sirrin

Gyara halaye

Ana tsammanin kowane Musulmi ya zama mai kyawawan halaye, amma a bangaren shirin zuwan Ramadana ya kamata kowane Musulmi ya ƙara zage dantse wajen gyara halayensa.

Hakan ya kama tun daga cikin gida a wurin iyali, maƙotaka da kuma cikin al'umma baki ɗaya. Zama cikakken Musulmi mai Imani na nufin ka zama mai kyawawan halaye.

Tsaftace zuciya da sassan jiki

Tsaftace rai na da matuƙar muhimmanci a watan Ramadan, ka tsaftace zuciyarka daga tunani mara kyau ko sheɗanci.

Haka nan ya kamata Musulmi ya tsare harshensa daga shiga maganganu marasa kyau, sannan yana da kyau ka rage kalle-kalle domin kare idonka daga kallon haram.

A wani labarin kuma Ramadan 2022: Shin kunsan kasashen Musulmai da za su kwashe awanni da yawa da awanni kaɗan suna Azumi bana

Biliyoyin al'ummar Musulmai a faɗin duniya na gab da shiga wata mai Albarka Ramadan na shekarar 2022.

Musulman wasu ƙasashe za su fuskanci dogon Azumi na tsawon awanni a bana, yayin da wasu kuma za su yi gajere.

Kara karanta wannan

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda ya kamata ya gaji Buhari a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262