Yan ta'adda sanye da Hijabi sun kai wa yan sanda Hari a Katsina, sun aikata babbar ɓarna
- Wasu tsagerun yan bindiga sanye da Nikabin mata sun kai hari wurin binciken ababen hawan yan sanda, sun kashe mutum ɗaya
- Kakakin yan sandan jihar Katsina yace lamarin ya faru lokacin da yan sandan ke bakin aiki a kan hanyar Jibia - Batsari
- Tuni kwamishinan yan sandan na jihar ya ba da umarnin jibge dakaru a yankin da lamarin ya faru a Daura
Katsina - Wasu yan bindiga sun farmaki yan sanda a wurin binciken ababen hawa a Daura, jihar Katsina, inda suka kashe ɗan sanda guda ɗaya.
Wata majiya mai ƙarfi a yankin da abun ya faru, ta ce yan ta'addan sun kawo harin sanye da Nikaf da Hijab domin boye fuskokinsu, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Da yake jawabi domin tabbatar da kai harin, kakakin hukumar yan sanda reshen Katsina, SP Gambo Isah, ya ce yan sanda na kan aiki aka farmake su.
A bayaninsa ya ce wasu dakarun yan sanda na cikin aikin duba ababen hawa a kan hanyar Jibia-Batsari lokacin da yan ta'addan suka mamaye su, suka kashe jami'i ɗaya.
Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?
Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa tuni kwamishinan yan sanda na jihar, Idris Dabban, ya ba da umarnin gaggawa na ƙara jibge yan sanda a yankin da abun ya faru.
Ya kuma umarci mataimakin kwamishinan yan sanda ya jagoranci ƙarin jami'an da za'a tura domin kame dukkan yan ta'addan da suka yi wannan aika-aika.
Wannan na zuwa ne yayin da yan arewacin Najeriya ke jimamin mummunan harin da yan ta'adda suka kai wa jirgin ƙasa a hanyar Abuja-Kaduna.
A wani labarin kuma Wani Magidanci ya ɗirka wa ɗiyarsa ciki har sau biyu, ya danna wa Matarsa ta sunnah saki
Wani mutumi a jihar Legas ya ɗirka wa ɗiyar cikinsa juna biyu, ya zubar sannan ya ƙara mata wani cikin karo na biyu.
Mahaifiyar yarinyar, wacce ta rabu da mutumin shekarun da suka shuɗe, ta fusata ta kai ƙorafinsa hannun yan sanda.
Asali: Legit.ng