Harin Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun harbi Kwamishinan lafiya na jihar Katsina

Harin Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun harbi Kwamishinan lafiya na jihar Katsina

  • Yan bindiga sun harbi Kwamishinan lafiya na jihar Katsina yayin harin da suka kai kan jirgin ƙasa a Kaduna
  • Wani makusancin Kwamishinan ya tabbatar da cewa kwamishinan yana kwance a Asibitin Sojoji a Ƙaduna
  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci hafsoshin tsaro su gaggauta nemo hanyoyin magance hanyar

Kaduna - Bayanan da muka samu yanzun sun nuna cewa yan ta'addan da suka kai hari kan jirgin kasa a hanyar Abuja-Kaduna sun jikkata Kwamishina na jihar Katsina.

Yan bindigan sun harbi kwamishinan Lafiya na jihar Katsina, Injiniya Yakubu Nuhu Ɗanja, yayin harin da suka kai jiya da daddare.

Ɗaya daga cikin makusantan kwamishinan a siyasa, Abubakar Rabiu Dabai, ya tabbatar da lamarin ga Legit.ng Hausa da yammacin yau Talata.

Malam Nasiru ya ziyarci Yakubu Nuhu.
Harin Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun harbi Kwamishinan lafiya na jihar Katsina Hoto: @GovKaduna
Asali: Facebook

Hadimin kwamishinan ya ce maharan sun harbi Uban Gidansu a Kafa, kuma yanzu haka yana kwance a wani Asibitin rundunar sojin Najeriya domin kula da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin Kasa: Shugaban Kungiyar Yan Kasuwan Najeriya Da Sakatare Suna Cikin Wadanda Aka Kashe

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubakar ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa:

"Eh, dagaske ne, harin jiya ya rutsa da kwamishinan lafiya na jihar Katsina, Injiniya Yakubu Nuhu Ɗanja, yanzu haka yana kwance a Asibitin Sojoji a Kaduna."
"Sun harbe shi a kafa, ba kamar yadda wasu ke cewa a hannu aka harbe shi ba, kuma a ɗazun gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya je ya duba lafiyar kwamishinan."

A jiya da daddare ne wasu ƴan ta'adda suka dasa wa jirgin dake aikin jigilar mutane a tsakanin Abuja zuwa Kaduna Bam, kuma suka zagaye shi bayan sun ta da Bam ɗin.

Mutane da dama sun rasa rayukansu, wasu kuma sun jikkata, a halin yanzun hukumomin tsaro sun bazama ceto waɗan da aka sace.

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da lamarin, yace ya kaɗu matuka da ya samu labarin faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wadanda suka jigata a harin jirgin Kaduna-Abuja

Buhari ya gana da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar nan baki ɗaya kan lamarin, ya kuma umarci su gaggauta ɗaukar mataki kuma su ceto wanda aka sace.

Haka nan ya jajantawa iyalan waɗan da suka rasu, sannan ya kara da Addu'a Allah ya tashi ƙafaɗun mutanen da suka jikkata.

A wani labarin kuma Mutanen Gombe sun kai ƙarar Pantami Kotu kan neman takarar gwamna a zaɓen 2023

Wasu tawagar mutane a jihar Gombe sun maka Ministan Sadarwa, Isa Pantami a gaban Kotu kan kujerar gwamna.

Shugaban ƙungiyar mutanen ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne domin tilasta masa ya nemi takarar gwamna a Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel