Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wadanda suka jigata a harin jirgin Kaduna-Abuja
- Farfesa Yemi Osibajo, ya hallara jihar Kaduna don ziryartar waɗanda farmakin jirgin ƙasa ya ritsa da su a daren Litinin
- Gwamnan jihar Kaduna da kwanishinan kula da lamurran tsaron cikin gida ne suka tarbi mataimakim shugaban kasar
- Osinbajo ya bayyana alhininsa, gami da lasar takobin kawo karshen hatsabiban dake addabar kasar
Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo ya hallara Kaduna don ziyartar waɗanda ƴan ta'adda suka kaiwa farmaki a jirgin ƙasan a daren Litinin.
Harin ya auku ne wuraren Kateri zuwa Rijana na jihar Kaduna.
An gano yadda ƴan bindiga sukayi dirar mikiya kan jirgin ƙasan, inda daga bisani suka kaiwa fasinjoji farmaki.
Osinbajo ya samu tarba daga hannun Nasir el-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, da Samuel Aruwan, kwamishinan kula da lamurran tsaron cikin gida.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Nayi matuƙar alhini da samun labarin yadda wasu ƴan ta'adda marasa tunani suka kaiwa mutane hari.
"Dolen mu ko don ƙasarmu da tarihinsu muyi yaƙi gami da cin galaba akan zabin dake kai hari ga al'umma. Bazasu karya kadarin mu ba. Zamu cigaba da kare kasarmu." a cewar Osinbajo.
Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja
A wani labari na daban, babu amo ba labarin manajan daraktan bankin manoma (BOA), Alwan Hassan tun lokacin da aka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna farmaki.
Hassan na ɗaya daga cikin fasinjojin da suka hau jirgin ƙasan Kadunan da aka kaiwa farmaki a ranar Litinin.
The Cable ta ruwaito yadda ƴan bindiga suka yi dirar mikiya ga jirgin ƙasan, inda daga bisani suna kaiwa fasinjoji farmaki.
Asali: Legit.ng