Ya cika burinsa: Labarin tsohon da ya samu takardar kammala sakandare yana da shekaru 101

Ya cika burinsa: Labarin tsohon da ya samu takardar kammala sakandare yana da shekaru 101

  • Burin wani tsoho dan shekaru 101 shi ne samun takardar kammala sakandare kasancewar bai da ita
  • Wannan yasa tsohon ya samu wata takardar kammala sakandare daga wata fitacciyar makaranta a yankinsu
  • Wannan lamari ya faro ne tun lokacin da ya samu matsala a danginsa har ya bar harkar karatu kwata-kwata

Virginia - Wani labari mai daukar hankali na dattijon da ya samu takardar kammala sakandare bayan tsawon jira na fiye da shekaru 80, Merrill Pittman Cooper ya ba mutane matukar sha'awa.

Dattijon dai ya halarci Kwalejin Storer da ke Harpers Ferry na West Virginia, daga 1934 zuwa 1938, amma ya bar makarantar kafin ya gama lokacin da danginsa suka kaura zuwa Philadelphia bisa wasu dalilai na kudi, in ji makarantar Jefferson County a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Dan sanda ya halaka rayuka 2 yayin da ya yi kokarin tserewa daga masu kama shi a Bauchi

Tsoho ya cika burinsa
Ya cika burinsa: Labarin tsohon da ya samu takardar kammala sakandare yana da shekaru 101 | Hoto: The Nation Newspaper
Asali: Twitter

Dalilin barinsa makarantar

An kafa Kwalejin Storer a shekara ta 1865 don tallafawa sababbin bayi da aka 'yantar bayan yakin basasa, a cewar Ma'aikatar Parking ta Amurka. Makarantar ta kasance daya daga cikin mabubbukar ilimi ga baki mazauna West Virginia.

Makarantar ta ilmantar da fiye da dalibai 7,000 kafin rufe ta a tsakiyar shekarun 1950. A kwalejin dai Mista Cooper yayi karatu, inda ya samu ilimin Latin, ilmin halittu, tarihi, Turanci, da ilimin lissafi.

Dalilin komawarsa makaranta

Duk da kasacewarsa bijirarre wa makaranta, Cooper ya ci gaba da samun nasara a harkarsa ta sufuri, inda a karshe ya zama mataimakin shugaban kungiyar sufuri, amma ya kan yi nadamar rashin samun takardar shaidar kammala sakandare.

A 2018, danginsa sun tuntubi makarantar Jefferson County game da cika masa burinsa.

Kara karanta wannan

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

Tare suka yi aiki tare da Harpers Ferry National Historical Park da Storer College National Alumni Association, da kuma Sashen Ilimi na West Virginia, don karrama Cooper saboda nasarorin da ya samu a Storer da kuma bayan haka.

A ranar 19 ga Maris, Cooper da danginsa sun halarci bikin yaye daliban na musamman, inda aka ba shi takardar shaidar karramawa.

Ga sanarwar da makarantar ta fitar:

Yadda saurayi mai shekara 18 ya zama Ango, ya auri ‘Yar shekara 16 a jihar Bauchi

A wani labarin, a ranar Juma’ar da ta gabata, aka ga wani aure da ba kasafai aka saba daura irinsa ba, saboda rashin yawan shekarun amaryar da angonta.

Daily Reality ta ce a kauyen Tilden Fulani, karamar hukumar Toro, jihar Bauchi, Muhammad Ahmad Salihu ya auri Amaryarsa Sumayyah Adam Ibrahim.

Majiya ta shaidawa jaridar cewa shekarun wannan Bawan Allah Muhammad Ahmad Salihu 18 a Duniya, ita kuma Sumayyah Adam Ibrahim ta na 16.

Kara karanta wannan

Dan kuka: Mata za ta share harabar makarantar su danta na tsawon watanni 6 bisa laifin jibgar malami

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.