Kano: An Kama Matashi Ɗan Shekara 25 Da Ya Halaka Tsohuwa Mai Shekara 80 Da Duka Ya Jefa Gawarta Cikin Rijiya

Kano: An Kama Matashi Ɗan Shekara 25 Da Ya Halaka Tsohuwa Mai Shekara 80 Da Duka Ya Jefa Gawarta Cikin Rijiya

  • Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama Nasiru Magaji mai shekaru 25 bisa zarginsa da halaka Habiba Abubakar, mai shekaru 80
  • Rahotanni sun nuna yadda ya yi shaye-shaye kafin ya lakada mata dukan tsiya, daga bisani ya jefa gangar jikinta cikin rijiya mai zurfi
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana hakan ta wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Asabar

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wani Naziru Magaji, mazaunin Kununu Yalwa Danziyal da ke karkashin karamar hukumar Rimin Gado cikin jihar.

Ana zarginsa da halaka wata Habiba Abubakar mai shekaru 80 sannan ya jefa gawarta cikin wata rijiya mai zurfin gaske, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

Kano: An Kama Matashi Ɗan Shekara 25 Da Ya Halaka Tsohuwa Mai Shekara 80 Da Duka Ya Jefa Gawarta Cikin Rijiya
An Kama Matashi Ɗan Shekara 25 Da Ya Halaka Tsohuwa Mai Shekara 80 Da Duka Ya Jefa Gawarta Cikin Rijiya a Kano. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana wa manema labarai hakan ta wata takardar ranar Asabar wacce ya gabatar wa manema labarai a Kano.

Ya amsa laifinsa, Ya ce shaye-shaye ya ke yi

Kamar yadda Nigerian Tribune ta nuna, wanda ake zargin ya kada baki ya ce:

“Sai da na yi shaye-shaye sannan na daketa, daga nan na jefata cikin rijiya mai zurfi. A ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2022 da misalin karfe 1:00 na rana, an samu korafi daga wani mazaunin kauyen Wangara da ke karkashin karamar hukumar Tofa cikin Jihar Kano.
“A ranar da misalin karfe 12 na rana wani Naziru Magaji mai shekaru 25 mazaunin kauyen Kununu Yalwa Danziyal da ke karkashin karamar hukumar Rimin Gado a Jihar Kano, ya lakada wa yayarsa, Habiba Abubakar mai shekaru 80 dukan tsiya. Sannan ya jefa ta cikin rijiya mai zurfi.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Sokoto: Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin ba tsagin Sani nasara

“Bayan kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Dikko ya samu bayanin, sai ya tura jami’ansa wadanda CSP Isiyaku Mustapha Daura ya jagoranta suka je wurin da lamarin ya auku.”

Ya ci gaba da shaida yadda suka yi gaggawa cirota daga rijiyar sannan aka zarce da ita babban asibitin Tofa inda likitoci suka tabbatar da cewa ta mutu.

Kwamishinan ya ce za su ci gaba da kama duk masu laifi a jihar

Kakakin ya ce yayin bincike, wanda ake zargin ya ce lafiyarsa kalau kuma shi ya zane tsohuwar mai shekaru 80 sannan ya jefa ta cikin rijiya. Ya ce sai da yasha kayan maye sannan ya yi aika-aikar.

Ya ci gaba da shaida cewa an mayar da matashin bangaren binciken masu laifi na musamman kuma za a tura shi kotu da zarar an kammala binciken.

A cewarsa, Kwamishinan ya ce masu laifi ba su da wurin buya a Jihar Kano. Kuma matsawar suna cikin jihar sai an kama su sannan an hukunta su.

Ya yi godiya ga mutanen kirkin Jihar Kano da kuma jami’an tsaro akan kokarinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164