Sojoji 25 Sun Samu Munanan Rauni a Yayin Da Motarsu Ta Yi Hatsari a Hanyarsu Na Zuwa Aiki
- An garzaya asibitin sojojin ruwa da sojoji 25 ranar Juma’a bayan wata babbar motarsu ta gabza karo a daidai tashar Beebosco da ke kan titin Murtala Mohammed a Calabar
- Sojoji 4 suna mawuyacin hali yayin da sauran 21 ciki har da mata 5 suka samu munanan raunuka a wurare daban-daban har da masu karaya a hannu da kafa
- Motar sojin ta bar hedkwatarsu da ke Calabar da misalin karfe 4:00 na yamma tana hanyar zuwa hedkwatarsu ta Ogoja da ke arewacin Jihar Cross River don yin wani aiki
Calabar - An yi gaggawar zarcewa da Sojoji 25 asibitin sojin ruwan Najeriya a ranar Juma’a da yamma bayan babbar motarsu ta gwabza karo da wata mota a tashar motocin Beebosco da ke kan babban titin Murtala Mohammed a Calabar, Vanguard ta ruwaito.
Bauchi: Miji Da Mata Da Wani Sun Mutu Yayin Da Tanka Man Fetur Ta Yi Taho Mu Gamu Da Motarsu, Wasu Sun Jikkata
Sojoji 4 suna kwance rai a hannun Allah, yayin da sauran 21, ciki har da sojoji mata 5 suka samu raunuka a wurare daban-daban, akwai wadanda idanunsu suka fashe, wasu kuma sun karya kafafu da hannaye.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babbar motar sojin ta bar hedkwata tsaron sojin kasa da ke Calabar da misalin karfe 4:00 na yamma suna hanyar zuwa wata barikin soji da ke Ogoja da rundunar sojin wacce wani manjo ya jagoranci tafiyar zuwa arewacin Jihar Cross River.
Direban ya sha giya ya yi tatil ne
Direban motar kamar yadda majiyar ta shaida, ya yi tatil da giya ne, hakan yasa ya dinga gudu inda suka isa tashar Beebosco har yazo gab da jerin wasu motoci sannan ya sa birki, daga nan motar ta hantsila kan wata motar kirar Sienna da aka ajiye ana tallarta.
Kamar yadda Emmanuel Ekpeta, wani dilan motoci ya shaida:
“Siennar ta taimaka, idan banda tana wurin da motar ta fada gadar ruwar Beebosco, hakan da ya fi zama babban bala’i.”
Ya ce wurin yana da santsi saboda ruwa yana zuba ta wurin, wanda hakan yasa direban bai lura ba, don haka ya kamata nan gaba a kula.
Ana kulawa da rayukan 25 a asibiti
Wani ganau ya shaida cewa:
“Sojojin sun fada cikin kwata ne hakan yasa suka fi wahala, kokon kanwunan wasu ya fashe yayin da goshin wasu ya yi ratsa-ratsa.”
John Eluu, mai Siennar da sojojin suka afka mawa, ya roki hukumar sojin akan ta taimaka masa ta hanyar biyansa saboda ta sana’ar yake cin abinci.
A asibitin sojin ruwan, inda aka zarce da sojojin da suka raunana, Dr Oyi, shugaban bangaren asibitin na gaggawa, ya ce an kai sojoji 25 amma daga bisani an wuce da 2 asibiti koyarwa na Jami’ar Calabar, UCTH, yayin da ake kulawa da sauran 23.
Captain H I Audu, wanda ya zanta da wakilin Vanguard ya ce hadari ne, kuma yanzu babban damuwarsu shi ne rayuwar sojojinsu.
Asali: Legit.ng