Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu
- Mahara sun kai hari wasu garuruwa da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna
- A yayin harin, an bindige mutane 50 sannan aka yi garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba
- Kakakin yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalinge, ya tabbatar da kai harin
Kaduna - Yan bindiga sun farmaki wasu garuruwa tara a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda suka kashe mutane 50 sannan suka yi awon gaba da wasu adadi da ba a sani ba, Daily Trust ta rahoto.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalinge, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce har yanzu hukumar taba riga ta tattara ainahin adadin mutanen da suka mutu ba a farmakin.
Jalinge ya ce:
“Har yanzu muna jiran cikakken bayani kan lamarin daga DPO na yankin Giwa da kwamandan Zaria."
Wani dan kungiyar yan banga a yankin Dillalai, Mansur Ibrahim, ya fada ma Daily Trust cewa yan bindigar sun kuma kona gidaje da ababen hawa sannan suka sace shanaye 100.
Ya ce:
“Kauyukan da abun ya shafa sune Dillalai, Zango Tama, Kaya, Barebari, Anguwan Bakko, Gidan Alhajin Kida, Kadanya da Durumi.”
“Yan bindigar sun kuma kona wani coci a kauyen Zangon Tama, duk a karamar hukumar Giwa.”
Ibrahim ya ce wasu da abun ya ritsa da su wadanda suka samu rauni sakamakon harbin bindiga na samun kulawar likitoci a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika-Zaria.
An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace
A wani labarin, mun ji cewa an ceto dan ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Ali Isa Pantami, da aka rahoto cewa an sace shi a jihar Bauchi, Daily Trust ta rahoto.
A cewar majiyoyi, an gano dan ministan ne a Dambam, daya daga cikin kananan hukumomin jihar Bauchi a ranar Juma'a a shigen jami'an tsaro.
Majiyar ba ta bayyana ko an biya kudin fansa ba.
Asali: Legit.ng