Daliban Najeriya sun ga ta kansu, SSANU da NASU sun bi ASUU, sun shiga yajin aiki

Daliban Najeriya sun ga ta kansu, SSANU da NASU sun bi ASUU, sun shiga yajin aiki

  • Da alamun daliban Najeriya dake karatu a jami'a su dade a gida, yayinda wasu ma'aikatun jami'o'i suka bi sahun Malamai
  • Kungiyar manyan maaikata SSANU da kungiyar NASU sun shiga sabon yaji
  • Kungiyoyin sun zargi gwamnatin tarayya da kin amsa bukatunsu wanda haka ya tilastasu daukan mataki

Kwamitin gamayya ta kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya (SSANU) da kungiyar ma'aikatan jami'o'i (NASU) sun alanta shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu.

Zasu fara wannan yajin ne ranar Litnin, 28 ga Maris, 2022, rahoton DailyTrust.

Wannan ya biyo bayan yajin da kungiyar Malaman jami'ar ASUU ke ciki yanzu haka.

Kungiyoyin SSANU da NASU yanzu sun bi sahun ASUU inda suka alanta shiga yajin aiki ranar Juma'a.

Kungiyoyin sun bayyana cewa sun yanke shawarar shiga yajin ne saboda gwamnatin Najeriya ta ki biya bukatunsu.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Sojoji sun samu gagarumar nasara kan Boko Haram/ISWAP a wani gumurzu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

SSANU da NASU sun shiga yajin aiki
Daliban Najeriya sun ga ta kansu, SSANU da NASU sun bi ASUU, zasu shiga yajin aiki Hoto: TheAbusite
Asali: UGC

A jawabin da shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim da Sakataren NASU, Peters Adeyemi, suka saki, suka ce:

"Dubi ga rashin kula da maida hankalin da gwamnati ta nunawa bukatunmu, mun umurtan mambobinmu a dukkan jami'o'in tarayya cewa su shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu fari daga daren Lahadi, 27 ga Maris, 2022."
"Wannan yajin aiki wajibi ne ga dukkan rassan NASU da SSANU da jami'o'in Najeriya da cibiyoyin ilimi maus alaka da jami'o'i."

Legit Hausa ta tuntubi mambar kungiyyar NASU a jami'ar birnin tarayya Abuja, Hajiya Laila inda ta tabbatar da cewa lallai tuni sun shiga yaji.

A cewarta:

"Mun shiga yajin aiki, sai mako mai zuwa zamu dawo. Yajin aikin na gargadi da tukun."
"Yanzu babu kowa a makarantar," kowa ya watse

Yajin Aikin ASUU: BUK Ta Umarci Duk Ɗaliban Da Ke Zama a Makaranta Su Kwashe Ya-Nasu Ya-Nasu Su Tafi Gida

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa: ‘Yan Majalisar Tarayya sun fusata da 'rainin wayon’ IGP da Ministocin Buhari

Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK ta umarci duk wasu dalibai da ke zama a cikin rassan makarantar guda biyu akan su kwashe ya-nasu ya-nasu su bar harabar makarantar zuwa ranar 20 ga watan Maris ko kafin nan.

Sannan jami’ar ta dakatar da duk wasu ayyukan da ake yi cikin jami’ar har sai makarantar ta dawo daga yajin aikin gaba daya, rahoton Daily Trust.

A wata takarda wacce sakataren watsa labaran jami’ar, Bala Abdullahi ya saki a maimakon magatakardar jami’ar, inda ya kula da cewa wannan matakin ya biyo bayan kara watanni 2 da ASUU ta yi na yajin aikin ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng