Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne
- Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Laraba ya fito fili ya ce yanzu haka yana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023
- Ya bayyana wa manema labarai na cikin gidan gwamnati bayan kammala taro da Buhari a fadar sa da ke Abuja, inda ya ce a APC zai tsaya takarar
- Kamar yadda ya bayyana, saboda tsabar dagewar sa wurin son cika burin na shi, har wadanda suke zawarcin kujerar tare sai da ya yi musu kamfen
Abuja - A ranar Laraba, Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya kori duk wata jita-jita, ya ce yanzu haka yana hararar tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Gwamnan ya yi hira da manema labarai na gidan gwamnati bayan ya kammala taro da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, The Punch ta ruwaito.
Yayin da aka tambaye shi idan ya hakura da takara, Umahi ya ce zai yiwu tunanin wani ne hakan. Amma a iya sanin sa, yana nan a kan bakar shi kuma masoyansa suna nan suna goya masa baya, yana ci gaba da kamfen kuma.
A cewarsa:
“Na samu nasarar tuntubar har wadanda suke da burin takara. Kuma hakan yana nuna cewa ina kan baka ta don ina ganin nufin Ubangiji ne. Duk abinda Ubangiji ya nufa babu mai hana wa.”
The Punch ta nuna wurin da Gwamnan ya ce hukuncin babbar kotun tarayya wacce ta tsige shi daga kujerar sa ta gwamna saboda sauya shekarar sa ya ci karo da hukuncin kotun koli akan wanda ke da kuri’u; jam’iyya ko kuma dan takarar.
Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP
Ya yi bayani akan tsige shi daga kujerar gwamna inda ya ce kuru’u na dan takara ne ba jam’iyya ba
Ya kara da cewa:
“Kun ga alamar damuwa tattare da ni? Kun gani, saboda Ubangiji ne ke tsara komai. Kuma ina ganin Ubangiji ya ba kotun damar yin hukunci, sannan ya ba wata kotun damar cewa kada in je ko ina, saboda mun sauya sheka, kuru’un na mu ne. Na damu kwarai saboda babbar kotun ta ce kuru’un na jam’iyya ne.
“Shiyasa duk da APC ce ta lashe zaben Jihar Bayelsa, bayan gano takardun mataimakin gwamnan suna da matsala aka ki ba su kujerar. Har ana goben ranar rantsarwa, kotun koli ta yanke hukunci inda ta nuna rashin cancantar dan takarar APC din wanda ya lashe zaben, saboda matsalar takardun mataimakinsa.
“Don haka idan kuru’u na jam’iyya ne, a ilimi irin na kotun koli, da dan takarar ya lashe zaben, sai jam’iyyar ta kawo wanda zai maye gurbin sa.”
Asali: Legit.ng