Allah ya zabi Tinubu ya gaji Buhari: Malaman addinin kirista a Arewa sun ce an yi musu wahayi

Allah ya zabi Tinubu ya gaji Buhari: Malaman addinin kirista a Arewa sun ce an yi musu wahayi

  • Malaman addinin Kirista daga yankin Arewa sun bayyana shirinsu na gudanar da taron addu’o’i mai ban mamaki don tabbatar da cikan burin Bola Tinubu na zama shugaban kasa
  • Burin shugaban na jam’iyyar APC na kasa na neman gadon karagar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 na ci gaba da daukar sabon salo
  • Kungiyar da fitaccen malamin coci, Bishop Sunday Garuba ya jagoranta ta ce burin Tinubu daga Allah ne, umarni ne daga sama

Gabanin zaben 2023, malaman addinin Kirista na Arewa sun shirya gudanar da wani katafaren taron addu’o’i na mutum miliyan daya domin rokon cikar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu.

A wani rahoto da Sahara Reporters ta fitar, kungiyar ta bayyana cewa a karshe burin tsohon gwamnan na jihar Legas na iya rugujewa idan ba tashi tsaye da addu'o'i ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Bishop Sunday Garuba, wanda ya jagoranci malaman ya bayyana cewa Allah ne ya umarce su. Ya ci gaba da cewa burin na Tinubu zai samun cikas daga miyagun da basu son alheri ga kasar nan.

Kiristocin Arewa sun hango zaman Tinubu a kujerar Buhari
Allah ya zabi Tinubu ya gaji Buhari: Malaman addinin kirista a Arewa sun ce an yi musu wahayi | Hoto: punchng.com
Asali: Depositphotos

Yayin da yake bayyana cewa Tinubu ne shugaban kasa na gaba da zai gaji Buhari, Garuba ya jaddada mahimmancin taron addu'ar ta kwana daya da suka shirya.

Malamin ya kuma bayyana cewa za su hada karfi da karfe domin karfafa muradin da Tinubu ke da shi domin amfanin Najeriya baki daya.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito shi yana cewa:

“A kasa da shekara guda, sabon shugaban kasa zai bullo don samar da wani sabon tsari ga al’umma. Bayan shafe sama da watanni uku muna addu'a da azumi sai da yawa, an bayyana mana cewa Bola Ahmed Tinubu ne jagoranmu na gaba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP

“Allah bai taba gazawa ba. Yakan cika alkawuransa, yana tabbatar da maganarsa fiye da sunansa. Muna da kwarin gwiwa cewa Asiwaju zai yi nasara.
“Amma wannan zai yiwu ne kawai idan muka yi roko a madadinsa. Kamar yadda muka sani, ruhi ne ke sarrafa jiki.”

Gwamnonin APC: Duk wanda Buhari ya zaba a taron gangamin shi za mu marawa baya

A wani labarin, gwamnonin jam’iyyar APC sun ce za su marawa duk wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi baya a taron gangamin jam’iyyar na kasa da za a gudanar a ranar Asabar 26 ga watan Maris.

Shugaban kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya jagoranci gwamnonin zuwa wata ganawa da shugaba Buhari, Leadership ta ruwaito.

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya shaida wa manema labarai bayan ganawar cewa za su goyi bayan duk wata hanya da za ta kai ga cimma matsaya wajen zaben shugabannin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdülaziz Yari

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.