Gwamnonin APC: Duk wanda Buhari ya zaba a taron gangamin shi za mu marawa baya
- A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC a fadin Najeriya
- A ganawar, ance sun tattauna kan abubuwan da suka shafi jam'iyya, inda gwamnonin suka nuna biyayyarsu ga Buhari
- Rahotanni da ke yawo sun nuna hotunan gwamnonin yayin da suka gama tattaunawa da shugaba Buhari a Abuja
Abuja - Gwamnonin jam’iyyar APC sun ce za su marawa duk wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi baya a taron gangamin jam’iyyar na kasa da za a gudanar a ranar Asabar 26 ga watan Maris.
Shugaban kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya jagoranci gwamnonin zuwa wata ganawa da shugaba Buhari, Leadership ta ruwaito.
Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya shaida wa manema labarai bayan ganawar cewa za su goyi bayan duk wata hanya da za ta kai ga cimma matsaya wajen zaben shugabannin jam’iyyar.
Jaridar Daily Sun ta ce, a watan da ya gabata ne shugaba Buhari ya ce yana goyon bayan tsarin da aka amince da shi na zaben ‘yan takarar mukaman jam’iyyar na kasa.
Ya bukaci gwamnonin da su hada kansu wajen tabbatar da tafiyar jam'iyyar yadda ya dace.
Hakazalika, gwamnoni da shugaba Buhari sun tattauna kan yadda taron gangami zai kasance a ranar 26 ga watan Maris din nan.
Wadanda suka halarci ganawar sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da gwamnoni 16; Kebbi, Plateau, Kogi, Yobe, Ogun, Kaduna, Ekiti, Ebonyi, Imo, Niger, Jigawa, Kwara, Zamfara, Nasarawa, Borno, da Osun.
Shirin taron gangami: Kwamiti ya tantance jiga-jigai 7 da ke neman kujerar shugabancin APC
A wani labarin, kwamitin tantancewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Gwamna Aminu Bello Masari ke jagoranta, ya tantance daukacin yan takarar shugabancin jam’iyyar na kasa su bakwai gabannin babban taronta da za a yi a ranar Asabar.
An gudanar da shirin tantance su ne a masaukin Gwamnan Katsina da ke babbar birnin tarayya Abuja.
Daily Trust ta rahoto cewa an fara shirin tantance yan takarar shugabancin jam’iyyar ne a daren ranar Talata har zuwa ranar Laraba inda aka tantance tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu da sauransu.
Asali: Legit.ng