Bidiyon mabaracin Legas dauke da bandiran kudi a jakunkuna ya janyo maganganu
- An kama wani mabaraci a birnin Legas da bandir-bandir na kudi a jakunkuna masu tarin yawa
- Duk da ba a kirga kudaden ba, amma daga abunda aka gani a bidiyon da yayi tashe, za a iya tabbatar da cewa kudi ne mai tarin yawa
- Bidiyon ya bar masu amfani da yanar gizo cikin mamaki, musamman wadanda ke ganin da kamar wuya mabarata su iya mallakar makudan kudade irin wannan
Legas - Wani mabaraci ya jefa mutane da dama cikin tsananin mamaki bayan an kama shi da bandir-bandir na nairori a jakunkuna.
An gano yadda kudaden ke da yawan gaske kuma sun kama tsakanin N1000 zuwa N100.
A halin yanzu bidiyon ne ke tashe a yanar gizo, wanda ke nuna makudan kudaden da mabaracin ya mallaka a jakunkunanshi.
An yi nasarar damke mabaracin, inda aka tilastashi ya zazzage dukkan jakunkunan da ya mallaka, inda aka ga kudi mai tarin yawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A duk lokacin da ya zazzage kowacce jaka, kudaden cigaba da fitowa suke.
Har zuwa lokacin da aka tattara labarin, ba a riga an kirga kudin ba, sai dai mutane da dama sun tabbatar da cewa, kudi ne mai tarin yawa, duba da yadda aka ga bandir-bandir masu yawan gaske.
Jamaa sun yi martani
Yayin da @mufasatundeednut. Ya wallafa bidiyon a Instagram, mutane da dama sun yi tsokaci daban-daban a kafafan sada zumuntar zamani.
@koffithaguru ya ce: "Menene takamaiman lafin da yayi. Idan da a ce kudaden nan na asusun bankin shi za ku sani ne? Kun dena rokon Ubangiji sa'a bayan wanda ya azurtaku da shi jiya? Meyasa a kullum mutanen mu suke cigaba da zama jahilai kuma munafukai ne? Ku fuskanci yan siyasan da suka talautaku gami da raunata ilimin ku. Shirme kawai!"
@officialrosie tayi tsokaci da: "Ba satar kudin yayi ba, kawai bara yayi kuma babu wani abu mara kyau idan ya tattali kudin da ya roki mutane, ko Ubangijin da muke roka sa'a kullum, bama denawa. Ina rokonsu da su rabu dashi da kudin shi."
@iamteiniryguy yayi tsokaci: "Akwai kudi a wannan harkar fa."
@wyterosey ya ce: "Kudin shi ne...watakila tarawa yake...ku kyale shi mana."
@bobbymaria ya ce: "Abun dariya, bara kasuwanci ne mai kyau. Kawai yana bukatar ka cire girman kai."
Asali: Legit.ng