Kudin Dangote sun kara yawa da N1.5bn yayin da aka kaddamar da kamfanin takinsa

Kudin Dangote sun kara yawa da N1.5bn yayin da aka kaddamar da kamfanin takinsa

  • Dangote ya ci gaba da samun makudan kudade kuma zai ci gaba da samu bayan kaddamar da katafaren kamfaninsa na takin zamani mafi girma a Afirka
  • Kamfanin takin na zamani shi ne mafi girma a Afirka kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da farashin taki ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya
  • ‘Yan sa’o’i kadan bayan bude kamfanin, wani sabon rahoto ya nuna cewa Dangote ya samu sama da Naira biliyan 1.5 kuma yanzu ya zama attajiri na 82 a jerin masu kudin duniya

A yau Talata 22 ga watan Maris ta kasance ranar farin ciki ga attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka; Aliko Dangote.

Sa’o’i kadan bayan bude wani sabon takinsa na zamani mai iya aikin tan miliyan 3 da aka gina kan kudi dala biliyan 2.5, sabbin bayanai daga cibiyar Bloomberg sun nuna cewa dukiyar Dangote ta haura da Naira biliyan 1.5 cikin ‘yan sa’o’i kadan.

Kara karanta wannan

Ziyarar Legas: Buhari ya dura masana'antar taki mafi girma a Africa, mallakin Dangote

Dangote ya kara arziki
Kudin Dangote sun kara yawa da N1.5bn yayin da aka kaddamar da kamfanin takinsa | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Sabon kamfanin taki na Dangote na zuwa ne a daidai lokacin da yakin kasar Ukraine ya jawo tashin gwauron zabi na iskar gas, wani muhimmin sinadarin samar da takin urea.

Reuters ta rahoto cewa Dangote a yayin bude kamfanin da shugaban kasa Muhammdu Buhari ya kaddamar ya ce zai fara fitar da takin har zuwa kasar Brazil, wadda ta dogara da kasar Rasha wajen shigo da taki. Har ila yau, takin zai kai ga Amurka, Indiya da Mexico.

Karin kudi ga Dangote

Kamfanin dai yana can a yankin Free Zone na Lekki a jihar Legas, kuma zai wadata dukkan manyan kasuwannin nahiyar Afrika; musamman yankin Sahara.

Yayin da babban bankin Najeriya ya hana shigo da taki daga kasashen waje a wani bangare na tsare-tsare da nufin bunkasa noman cikin gida, hakan na nufin manoman Najeriya za su kara dogaro da masana'antar takin ta Dangote.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira jihar Legas kaddamar da ayyuka

Abokan fafatawar Dangote a Najeriya

Ba Dangote bane kadai zai cinye kasuwar taki a Najeriya, saboda akwai kamfanin Notore da ke jihar Rivers da ke da karfin samar da metric tonne 500,000 a duk shekara na nau'in takin urea.

Akwai kuma Indorama Eleme Petrochemicals Ltd mallakar kasar Singapore, wanda ke shirin ninka yawan samar da takin urea a shekara zuwa tan miliyan 2.8.

Tsabar kudi: Dangote ya tsallake matsayi mai girma, ya dara attajirai 429 da ake ji dasu a duniya

A wani labarin, attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, kuma shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote na Najeriya, ya zuwa ranar Laraba, 9 ga Maris, 2022 ya zama mutum na 71 mafi arziki a duniya sabanin matsayinsa na 100 da a farkon 2022.

A yanzu dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 20.1, bayan da ya tara dala miliyan 914 (N380bn) cikin kankanin lokaci, a cewar rahoton kididdigar hamshakan masu kudi na Bloomberg.

Kara karanta wannan

TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido

Hamshakin attajirin nan dan kasar Afrika ta kudu Johann Rupert yana matsayi na 221 a jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya, inda arzikinsa ya kai dala biliyan 9. Hakan ya nuna cewa, Dangote ya ninka shi sau biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.