Jibgegiyar Matata Tana Lakaɗa Min Duka Kuma Bata Nadama, Miji Ɗan Shekara 60 Ya Roƙi Kotu Ta Kashe Aurensa

Jibgegiyar Matata Tana Lakaɗa Min Duka Kuma Bata Nadama, Miji Ɗan Shekara 60 Ya Roƙi Kotu Ta Kashe Aurensa

  • Wani magidanci mai shekaru 60 zuwa 69 ya yi karar matarsa a kotu yana neman a datse igiyar auren da ke tsakaninsu
  • John Anya ya shaida wa alkali cewa matarsa wacce ke da tsawo da girman jiki tana masa duka kuma ba ta nadaman yin hakan
  • A bangarenta, matar ta musanta cewa tana dukan mijinta, tana mai cewa shine ya ke dukanta kuma neman mata ya ke yi kuma baya bata isashen kudin cefane

Legas - Wani magidanci mai shekaru 60 zuwa 69, John Anya, a ranar Talata, ya roki wata kotun kwastamare da ke zamanta a Legas ta raba aurensa da matarsa mai shekaru 33, Egobeke.

A karar da ya shigar, Anya, dan kwangila mazaunin gida mai lamba 7, Unity Avenue, Akesan, ya nemi sakin ne kan dalilin cewa matarsa ta lakada masa duka kuma bata yi nadama ba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Jibgegiyar Matata Tana Lakaɗa Min Duka Kuma Bata Nadama, Miji Ɗan Shekara 60 Ya Roƙi Kotu Ta Kashe Aurensa
Matata Tana Lakaɗa Min Duka Kuma Bata Nadama, Miji Ɗan Shekara 60 Ya Roƙi Kotu Ta Kashe Aurensa. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"Matata bata da hali mai kyau. Tana nuna min halinta idan bani da kudi da zan bayar don cefane. Duka ta ke min.
"Sai da na gudu daga gida na koma zama a coci don tsira da rayuwa ta. Ta taba yin kokarin ta shake ni in mutu.
"Duba tsawonta da girmanta. Yanzu ka yi tsammanin ta danne ni da nufin halaka ni," ya shaida wa kotu.

Ya kuma yi zargin matar ta cinye jarin sana'ar da ya bata.

"Bata da tattali. Tana hure wa yayana kunne ba su kauna na. Na gaji da halinta, ina son a raba mu," ya shaida wa kotu.

Martanin matan mai suna Egobeke

Wacce aka yi kara, Egobeke, yar kasuwa ta shaida wa kotun cikin hawaye cewa bata son sakin kuma duk abin da mijin ya fada ba gaskiya bane.

Kara karanta wannan

Jarumai 5 da ke jan zarensu a masana'antun Kannywood da Nollywood cike da kwarewa

"Wacce macen kirki za ta so a danganta ta da saki. Bana son saki, kafin mu yi aure, an fada min cewa zan fuskanci kallubale kuma na yarda zan jure.
"Abin da na jure a auren nan ya isa. Ban san abin da yasa miji na ya ke min sharri ba," ta shaida wa kotu.

Ta shaida wa kotu cewa mijinta ya mata abubuwa marasa dadi da ba za ta iya fadi ba.

"Duk wannan matsalar ya taso ne saboda yana soyayya da wasu mata uku. Daya daga cikinsu kawa ta ce.
"Bai san na san abin da ya ke aikatawa ba, yana neman matan banza," a cewar ta.

Ta kuma shaida wa kotun cewa N1000 ya ke bata a matsayin kudin cefane a kullum duk da cewa suna da yaya biyar.

"Ya ce ina dukansa? Don Allah ka ga tabo a jikinsa? Amma duba jiki na za ka tabbai na dukan da ya ke min."

Kara karanta wannan

Kano: Matashiyar budurwa mai shekaru 14 dake sana'ar saka tayils

Alkalin kotun, Koledoye Adeniyi, ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Maris.

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

A wani labarin, Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a Oyo ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ɗirka wa matarsa ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ƴaƴa uku da bai da tabbas nasa ne, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164