Delta: 'Dan Sanda Ya Bindige Wani Mai Hako Karafa, Aminu, Saboda Ƙin Bashi Rashawar N1,000 Kacal
- Ana zargin dan sanda a Jihar Delta da halaka wani mai hako karfe, Aminu saboda ya hana shi rashawar N1,000 wacce ya bukata a hannun sa
- Kamar yadda majiyoyi suka nuna, yayin da dan sandan ya matsa wa Aminu akan kudin wanda yake amsa wurin sa kullum, ya amince zai biya shi N500 sau biyu
- Wannan lamarin ne ya harzuka dan sandan inda ya fito da bindiga take anan ya harbe shi, wanda take anan ya fadi ya mutu
Jihar Delta - Wani dan sanda da ke aiki da ofishin ‘yan sanda na Agbor ya harbi wani mai hako karafa, mai suna Aminu bisa zargin kin ba shi rashawar N1,000, The Punch ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ika ta kudu da ke Jihar Delta.
The Punch ta tattaro bayanai akan yadda dan sanda ya ke amsar kudade kullum daga hannun mamacin, wanda a ranar ya ce bai yi cinikin ko sisi ba.
Har Aminu ya amince zai yi masa biya biyu amma ya halaka shi
Majiyoyi daga yankin sun sanar da wakilin The Punch cewa dan sandan ya ci gaba da matsawa har marigayi Aminu ya amince zai biya shi N500 sau biyu, lamarin da ya hassala dan sanda daga nan ya ciro bindiga ya fara barazanar harbinsa.
A cewar majiyar:
“Yayin da suke ci gaba da ka ce-na ce, dan sandan ya yi tunanin Aminu ba ya son biyan kudin ne, hakan yasa ya fara yi masa barazana. Take a wurin ya harbe shi da bindiga wanda ya yi ajalin sa a wurin.”
An fara zanga-zanga akan kisan Aminu
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, DSP Bright Edafe, ya ce bai san komai ba dangane da lamarin, amma ya ce zai tuntubi wakilin The Punch idan ya samu labari.
Kawo lokacin rubuta wannan rahoton, kakakin bai sanar da komai ba dangane da lamarin.
Sai dai, mambobin kungiyar ci gaban Arewa, APF, reshen Ika, sun fara zanga-zanga a ofishin ‘yan sanda da ke Agbor, Agbor-Obi, suna bukatar a yi adalci ga wanda aka halaka, kasancewar shi ma dan kungiyar ne.
An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona
A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.
Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.
Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.
Asali: Legit.ng