Diyar sanusi Lamido ta bayar da hakuri kan furucin da ta yi game da Larabawa
- Shahida Sanusi Lamido ta yi karin bayani a kan cewa da ta yi Larabawa na nuna wariyar launin fata
- Diyar tsohon sarkin na Kano ta ce ba nufinta ta yi batanci ga Larabawa sannan ta nemi duk wanda batun ya shafa ko ya batawa rai da ya yi hakuri
- Ta jadadda cewa lallai akwai mutane masu karamci sosai a cikin jinsin Larabawan
Diyar tsohon sarkin Kano, Mai martaba Muhammadu Sanusi II, Shahida ta bayar da hakuri kan cewa da ta yi Larabawa na nuna wariyar launin fata.
Shahida dai ta bayyana halin da ta riski kanta tare da wasu Larabawa a Saudiyya yayin da ta ke amsa tambayoyi a kan shafinta na sada zumunta.
Harma ta ce hatta ga mai gadinsu ya nuna masu wannan dabi’a domin a cewarta baya amsa gaisuwarsu.
Bayan wannan wallafa tata ya +*+hau kanen labarai, sai ta sake komawa shafinta na Instagram domin bayar da hakuri a kan kudin goro da ta yi.
Ta yi bayanin cewa ta hadu da Larabawa masu karamci da dama sannan kuma ta kara da cewa kawai ta yi magana ne game da "wasu al'amura na wariyar launin fata.”
Ta ce:
“Na yi mamaki yadda wani sharhi da na yi a shafina na Instagram wanda nake tsammanin ba zai wuce sa’o’i 24 ba ya shiga wasu shafukan yanar gizo sannan kuma a yanzu ya shiga kanen labarai. Don haka nake karin bayani da ban hakuri. Wannan ya bani mamaki kuma ina mai bayar da hakuri ga duk wanda wallafan ya shafa ko ya bata masa rai. Ganganci ne.
“Ba wai ina nufin dukka Larabawa ne ke nuna wariyar launin fata ba, tabbas ba haka lamarin yake ba. Ina da kawaye larabawa haka ma yawancin mu suna da su. Kuma duk mun san mutanen da ba abokanmu ba ne amma kuma mutane ne masu karamci, kudin goro da na yi shine kuskurena.
“Na yi magana game da kebantaccen lamari na wariyar launin fata kuma ban shiga cikinsu ba: A zahirin gaskiya: A makaranta: wata ma’aikaciya a makarantar diyata- ita kadai ce ta nuna mana wariyar launin fata (shekaru biyu da suka gabata) kuma a karshen shekara na makarantar, ta tafi. Ban taba kai kararta ba saboda mu'amalar da muke yi kadan ce kuma gaba daya ni na guje wa haduwa (kuskure na) amma makarantar ta lura da wani abu game da ita kuma ta sallame ta.
"Duk da haka, kamar yadda na ce ban fuskanci wariyar launin fata kai tsaye ba kuma yawanci sun kasance abubuwan da ke nuna alamu na wariyar launin fata a mizanin tunani - don haka watakila ba wannan ba ne nufin. Kasar Saudiyya tana da fadi sosai kuma da yawa daga cikin larabawan da mutum ke mu'amala da su a nan ba asalin yan Saudiyya bane. Kuma watakila ma ba lallai ne su kasance larabawa ba.
"Ina mai bayar da hakuri daga zuciyata. Na gode da fahimtar ku."
Diyar tsohon Sarkin Kano Sanusi II da ke Saudi ta bayyana wani mummunan halin Larabawa
A baya mun ji cewa, daya daga cikin ‘ya ‘yan Mai martaba Muhammadu Sanusi II, Shahida Sanusi ta zargi Larabawa da nuna bambanci da wariyar launin fata.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Shahida Sanusi mai zama a Saudi Arabia ta na zargin mutanen kasar Larabawa da nunawa sauran jama’a bambanci.
Hajiya Shahida Sanusi ta jefi Larabawa da wannan zargi ne yayin da ta ke amsa tambayoyin mutane a kan shafinta na sada zumunta na Instagram.
Asali: Legit.ng