Diyar tsohon Sarkin Kano Sanusi II da ke Saudi ta bayyana wani mummunan halin Larabawa

Diyar tsohon Sarkin Kano Sanusi II da ke Saudi ta bayyana wani mummunan halin Larabawa

  • Shahida Sanusi Lamido ta dura kan Larabawa, ta ce su na da nunawa bakake wariyar launin fata
  • Babbar ‘diyar tsohon Sarkin Kano ta bayyana haka ne wajen amsa tambayoyi a dandalin Instagram
  • Tsohuwar gimbiyar Kano ta bada labarin irin kalubalen da su ke fuskanta a kasar Saudi Arabiya

Saudi - Daya daga cikin ‘ya ‘yan Mai martaba Muhammadu Sanusi II, Shahida Sanusi ta zargi Larabawa da nuna bambanci da wariyar launin fata.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Shahida Sanusi mai zama a Saudi Arabia ta na zargin mutanen kasar Larabawa da nunawa sauran jama’a bambanci.

Hajiya Shahida Sanusi ta jefi Larabawa da wannan zargi ne yayin da ta ke amsa tambayoyin mutane a kan shafinta na sada zumunta na Instagram.

Wani ya tambayi ‘diyar tsohon Sarkin ko Larabawa su na da wannan hali na nunawa bakake wariya, kuma shin ta taba fuskantar wannan matsalar.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC, Bawa, ya yi martani kan kamen tsohon gwamna, zargin cin zarafinsa a siyasance

"Haka Larabawa su ke"

Da take bada amsa, sai ta ce shakka-babu, Larabawa su na da wannan dabi’ar a Saudi Arabiya.

Tsohuwar gimbiyar ba ta tsaya a nan ba, ta bada labarin irin abin da ya faru da ita a kasar Saudi Arabiya, duk da cewa addini ya haramta nuna bambanci.

Diyar tsohon Sarkin Kano
Shahida Sanusi Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC
“Maganar gaskiya su na da shi. An nuna mani, amma gaskiya ya fi shafar ‘diyata (ni ba na hulda da su sosai, har da zan sani).
“Amma babu shakka an nuna mana wariyar launin fata, har a masallaci da kuma filin wasa a gaban gidanmu.”
“Har a makarantar ‘ya ta, su biyu ne kadai bakake; da farko nayi tunanin ba haka ba ne, amma daga baya na fahimta.”
“Abin ban haushi, ka da a jawo in fara bada labaran da na ji daga bakin wasu mutane.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19

“Kai har mai gadinmu ‘Haris’ ya nuna mana wariyar launin fata a farkon zuwanmu. Ba zai amsa gaisuwar mu ba. Hauka ne!”

- Shahida Sanusi Lamido

Auren wuri a Arewa

A baya kun ji cewa mutane su na ta surutu yayin da aka ji labarin wani atashi mai shekara 18 ya auri ‘Yar shekara 16 da haihuwa a garin Tilden Bauchi.

Wannan ba bakon abu ba ne a Arewacin Najeriya amma akwai masu ganin Muhammad Ahmad Salihu da Sumayyah Adam Ibrahim sun yi auren wuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng