'Yan Bindiga Sun Kashe Malami Da Wasu Mutane Huɗu a Kaduna
- ‘Yan bindiga sun halaka wani malamin makaranta tare da mutane 4 a Layin Lasan Tabanni da ke Karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna
- Sannan ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wasu mutane 16 a kauyen Dogon Dawa, Layin Mahuta da Tabanni da ke gabashin karamar hukumar
- An samu wannan bayanin ne ta wata takarda wacce kungiyar jami’an tabbatar da tsaro da shugabanci na kwarai na Birnin Gwari wacce shugabanta, Ibrahim Abubakar Nagwari ya sa hannu
Jihar Kaduna - ‘Yan bindiga sun halaka wani malami da wasu mutane hudu a layin Lasan Tabanni da ke cikin karamar hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Maharan sunyi garkuwa da mutane 16 a Dogon Dawa, Layin Mahuta da kauyen Tabanni da ke gabashin karamar hukumar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An samu wannan bayanin ne a wata takarda wacce jami’an tabbatar da tsaro da shugabanci na gari na Birnin Gwari suka saki, wacce shugabanta, Ibrahim Abubakar Nagwari ya sanya hannu.
Kungiyar ta ce makamancin haka ya maimaita kansa cikin kwana 4, tsakanin ranar 14 ga watan Maris na shekarar 2022, zuwa ranar 19 ga watan Maris.
Sun kai farmaki wasu kauyakun daban
A cewar kungiyar, a ranar 14 ga watan Maris, wani Haruna Tanko Dogon Dawa da wasu mutane biyu sun rasa rayukan su yayin da ‘yan bindigan suka kai farmaki Dogon Dawa da ke titin Zaria, rahoton Daily Trust.
Kamar yadda Ibrahim Abubakar Nagwari ya ce:
“An yi garkuwa da wasu mutane 8 duk a kauyen. A Layin Mahuta (Tabanni), wani Abdullahi Abubakar, wani malami ya rasa ran sa a Layin Lasan, kan layin Tabanni a ranar Laraba, 16 ga watan Maris din 2022.
“A ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, ‘yan bindiga sun halaka wani tsoho mai shekaru 70 sannan sun yi garkuwa da mata 7 a Layin Mahuta Tabanni. Sannan an sace wasu mutane 2 a tsohuwar Tabanni.”
Shugaban kungiyar ya kara da cewa a Randagi kuwa, ‘yan bindiga sun saki mutane 32 cikin 46 bayan makwanni uku da suka yi garkuwa da su a Unguwar Bula da Ijinga bayan sun biya N16m a matsayin kudin fansa.
Kungiyar ta roki jami’an tsaro akan yin gaggawar amsa kira daga kauyaku
Kungiyar ta ci gaba da rokon jami’an tsaro akan yin gaggawar amsa kiran musamman a gundumar Dogon Dawa, Kuyello, Tabanni da Kutemashi da ke Birnin Gwari.
Wani shugaban matasa da ke gundumar Kuyello, Baban Yara, ya ce marigayin malamin kawunsa ne, inda ya kwatanta shi a matsayin mutumin kirki.
Shugaban karamar hukumar, Hajiya Ummah K. Ahmed ta tabbatar da batun kisan malamin inda ya ce wani mutum daya ya raunana.
Borno: Sojoji Sun Gasa Wa Ƴan Ta'adda Aya A Hannu, Sun Kashe 10 Sun Ƙwato Bindigu Masu Harbo Jiragen Sama
A cewarta:
“Na dai san batun kisan malamin da kuma wani mutum daya wanda ya ji rauni sakamakon harsashin bindiga, kuma na tura shi asibiti don kulawa da lafiyarsa.
“Ba na da masaniya akan batun garkuwa da mutane da sauran ta’addancin da kungiyar ta fadi.”
Asali: Legit.ng