Sheikh El-Zakzaky: Jami'an Tsaro Sun Buƙaci Matata Ta Tuɓe Tufafinta

Sheikh El-Zakzaky: Jami'an Tsaro Sun Buƙaci Matata Ta Tuɓe Tufafinta

  • Shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya yi zargi jami'an tsaron Najeriya sun nemi matarsa ta tube tufafinta
  • Sheikh Zakzaky ya ce hakan ya faru ne a lokacin da jami'an tsaron suka kawo hari a gidansa a shekarar 2015 inda suka kashe daruruwan mutane
  • Babban malamin ya bayyana cewa a yayin harin an kashe masa yayansa hudu da yayan riko shi kuma an masa mummunan rauni a cinyarsa inda ya yi ta jinya na watanni

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Musulmai mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya, IMN, ya zargin cewa jami'an tsaron da suka bude wuta a kansa da mabiyansa sun nemi matarsa ta cire tufafinta.

Ya furta hakan ne cikin wata hira ta musamman da ya yi da Shugaban Sashen Hausa na BBC Hausa, Aliyu Tanko.

Kara karanta wannan

Putin ya tsure, ya tattara ma’aikata 1000 ya kora saboda tsoron a sa masa guba a Rasha

Sheikh El-Zakzaky: Jami'an Tsaro a Najeriya Sun Buƙaci Matata Ta Tuɓe Tufafinta
Sheikh El-Zakzaky: Jami'an Tsaro a Najeriya Sun Nemi Matata Ta Tuɓe Tufafinta. Hoto: BBC Hausa
Asali: Twitter

A yanzu kimanin shekaru shida kenan bayan rikici tsakanin yan Shi'a masu biyaya ga Sheikh Ibrahim Zakzaky da Sojojin Najeriya, kan zargin da sojojin suka yi na cewa yan Shi'a sun tare musu hanya a Zaria.

A cewar Zakzaky, wasu jami'an tsaro su hudu dauke da makamai ne suka kutsa karamin dakin da ya ke tare da iyalansa suka ta yin luguden wuta a 2015.

Jami'an tsaro sun bukaci matata ta cire kayanta, amma ta ce ba za ta cire ba, Zakzaky

Ya ce jami'an tsaron sun halaka daruruwan mutane kafin suka kai gare su, "suna bude (daki) suka gan mu suka ce ga wasu nan; ita matata...suke fada mata ta cire tufafinta, da ta ce ba za ta cire ba suka ce a bude wuta."

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Ya cigaba da cewa bayan jami'an tsaron sun bude wuta ne sai dakin da suke ciki ya turnike da hayaki da kaurin harsashi kamar yadda BBC Hausa ta rahoto.

An kashe min yayana hudu da yayan riko da wasu mabiya na, El-Zakzaky

Har wa yau, ya ce akwai yayansa tare da shi da matarsa a dakin, inda sojojin suka harbi ma dansa mai shekara 15 harsashi ta shiga kokon kansa, sun kashe yayansa hudu da yayan riko sannan sun dagargaza masa cinya.

Sheikh Zakzaky ya ce bayan kura ta lafa ne aka kai shi da iyalansa asibitin sojoji kuma daga baya aka sauya wani asibitin inda ya kwashe kimanin wata uku yana jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164