Da Duminsa: Kotu ta umarci AGF ya cire sashen da Buhari ya nema a cire daga dokar zabe

Da Duminsa: Kotu ta umarci AGF ya cire sashen da Buhari ya nema a cire daga dokar zabe

  • Wata kotu da ke zamanta a Umuahia ta bayar da umarnin cire sashe na 84(12) na sabon kundin dokar zabe na Najeriya
  • Kotun ta bayar da wannan umarni ne bayan da wani Nduka Edede na jam’iyyar AA ya shigar da kara inda ya ce sashin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar
  • A cewar kotun, duk wani tanadi na doka da ta yi hannun riga da Kundin Tsarin Mulki kamar sashe na 84 (12) na dokar zabe ya zama aikin banza

Umahia, Abia - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Umuahia, babban birnin jihar Abia a ranar Juma’a, 18 ga watan Maris, ta umurci ministan shari'a, Abubakar Malami, da ya shafe sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Hukuncin kotu kan dokar zabe ta Buhari ya raba kan Sanatoci

Channels Tv ta rawaito cewa, umarnin kotun ya biyo bayan bukatar da shugaban Buhari ya mika wa majalisar dokokin kasar na a soke wani bangare na dokar da ta haramta wa mambobin majalisar zartaswa tsayawa takara ba tare da yin murabus ba.

Kotu ta ba da umarnin soke sashin dokar zabe
Da Duminsa: Kotu ta umarci AGF da ya cire sashen da Buhari ya nema a cire daga dokar zabe | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A hukuncin da ta yanke, babbar kotun ta bayyana cewa ana bukatar masu rike da mukaman siyasa su yi murabus daga mukamansu ne kawai kwanaki 30 kafin zabe ba da wuri ba kamar yadda sashe na 84(12) na dokar zabe ya tanada.

Nduka Edede, wani mai kada kuri'a a jihar Abia kuma mamba a jam'iyyar Action Alliance (AA) ne ya shigar karar gaban kotun.

Jam’iyyar ta AA na daya daga cikin jam’iyyun siyasa da suka kalubalanci AGF kan wannan bangare na dokar zabe.

Kara karanta wannan

Kotu ta sake ba Sowore gaskiya, ta ci DSS tara saboda cafke ‘Dan gwagwarmaya tun 2019

Dalilan da kotu ta fitar

Da take warware sashe, kotun ta ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa saboda ya saba wa tanadin sashe na 66 (1) (f), 107 (1) (f), 137 (1) (f) da 182 (1) (f) ) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da ya tanadi murabus akalla kwanaki 30 gabanin zabe.

Kotun a cikin hukuncin da ta yanke ta ce duk wani tanadi na wata doka da ta saba da sharuddan kundin tsarin mulkin kasar, to ba shi da tushe balle makama.

Ya kara da cewa majalisar ta wuce gona da iri ta hanyar amincewa da irin wannan dokar da ta saba wa kundin tsarin mulki wanda shi ne ka’idar kotu.

Dokar zabe: Tashin hankali yayin da majalisa ta yi watsi da dokar zabe ta Buhari

A baya jaridar The Nation ta ruwaito cewa, majalisar dattawa a ranar Laraba ta yi watsi da kudirin doka da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar na neman gyara dokar zabe ta 2022.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC

Kudirin doka mai taken:

“Kudirin dokar da zai gyara dokar zabe ta 2022 da kuma abubuwa masu alaka, 2022,” Sanatoci sun yi watsi da shi, lamarin da ya dakatar da karatun kudurin na biyu.

Kudurin dokar ya tsallake karatu na farko a ranar Talata duk da umarnin da kotu ta bayar na hana Majalisar Dattawa yin aiki akansa.

Kafin Majalisar Dattawa ta fara nazarin kudirin a ranar Laraba, Sanata Adamu Aliero, yayin da yake karanto doka ta 52 (5) na Majalisar Dattawa, ya bukaci Shugaban Majalisar da ya yi watsi da shawarar duba ga kudirin.

A wani labarin, gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja a ranar Juma'a ya ziyarci takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni, kuma shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC na kasa (CECPC).

Idan baku manta ba, rahoton jaridar Tribune ya bayyana cewa, gwamna Buni da Bello sun shiga ganawa bayan dawowar Buni.

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

A cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na Buni, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar a Damaturu, ya ce Bello ya jagoranci sauran mambobin tawagar CECPC wajen tarbar Buni a dawowarsa gida daga jinyar da ya yi a Dubai, PM News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.