Rikicin APC: Abubuwan da Gwamna Buni da Bello suka tattauna a ganawarsu
- Gwamnan jihar Yobe ya dawo Najeriya kwanaki kadan bayan ya tafi kasar waje domin duba lafiyarsa
- A wani sako da ya wallafa a Facebook, Buni ya mika godiyarsa ga takwaransa na jihar Neja wanda ya rike mukamin shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC a madadinsa
- A halin yanzu dai sun gana a Abuja, kuma daraktan yada labarai na Buni, Alhaji Mamman Mohammed ya bayyana yadda ganawar tasu ta kasance
Abuja - Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja a ranar Juma'a ya ziyarci takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni, kuma shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC na kasa (CECPC).
Idan baku manta ba, rahoton jaridar Tribune ya bayyana cewa, gwamna Buni da Bello sun shiga ganawa bayan dawowar Buni.
A cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na Buni, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar a Damaturu, ya ce Bello ya jagoranci sauran mambobin tawagar CECPC wajen tarbar Buni a dawowarsa gida daga jinyar da ya yi a Dubai, PM News ta ruwaito.
Dalilin haduwar Buni da Bello
Bello, wanda ya wakilci kujerar Buni ta CECPC a lokacin jinyar, ya ce kwamitin ya ziyarci Buni ne domin yi masa bayani kan al’amuran da suka shafi jam’iyyar yayin da shi (Buni) ba ya nan.
Ya ce bisa mika mulki da Buni ya yi masa, kwamitin ya fara gudanar da shirin taron gangamin APC na ranar 26 ga Maris.
Taron gangamin APC na nan daram, inji Buni
Da yake mayar da martani, Buni ya yabawa mambobin kwamitin bisa goyon baya da hadin kai da suka baiwa Bello yayin da shi ba ya kasar.
Ya ba da tabbacin cewa ranar taron gangamin na ranar 26 ga Maris tana nan daram kuma ya nemi goyon baya daga dukkan ‘yan jam’iyyar domin samun nasarar gudanar da taron.
Buni ya yabawa mambobin kwamitin bisa jajircewarsu wajen tabbatar da manufofin jam’iyyar da kuma hadin kai domin samun nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Yadda aka yi kutun-kutun, aka tunbuke Sakataren APC kafin Mala Buni ya dawo daga Dubai
A wani labarin, takarda ta fito inda aka ga cewa an sauke Sanata John James Akpanudoedehe daga kujerar sakataren kwamitin CECPC na jam’iyyar APC na kasa.
Jaridar Premium Times ta kawo rahoto a game da sila da duk yadda aka bi, aka yi waje da John James Akpanudoedehe wanda shi ne na biyu a jam’iyyar APC.
An dauki matakin tsige sakataren ne a lokacin da ‘yan kwamitin rikon kwaryan jam’iyyar suka yi wani taro kwanakin baya a sakatariyar APC da ke birnin Abuja.
Asali: Legit.ng