Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obiano garin tserewa Amurka

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obiano garin tserewa Amurka

  • Sa'o'i kadan bayan hukumar EFCC ta kama tsohon gwamna Willie Obiano a Legas, wani rahoto ya zayyana wasu laifuffukan da ake zargin sun kai ga kama shi
  • A cikin wasu bayanai, rahoton ya bayyana cewa an kama tsohon gwamnan na jihar Anambra ne bisa zargin karkatar da makudan kudade sama da N17bn na Paris Club
  • A halin da ake ciki, kafin a kama shi, EFCC tun a watan Nuwamba 2021 ta sanya Obiano a cikin jerin sunayen wadanda take zuba musu ido

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a daren Alhamis, 17 ga watan Maris, ta kama tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.

An kama shi ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas, sa’o’i kadan bayan da ya mika mulki ga magajinsa, Charles Soludo a hukumance.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo

Yadda aka kama gwamna Obiano
Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna a ranar da ya bar ofis | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan yana kokarin shiga jirgin ne domin ya shilla Amurka lokacin da hukumar ta EFCC ta damke shi.

Yayin da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kama Obiano, bai yi karin bayani kan dalilin da ya sa aka kama shi ba.

Duk da haka, tsohon gwamnan na Anambra yana cikin jerin wadanda EFCC ke sanya masu ido na tun ranar 15 ga Nuwamba, 2021.

Har ila yau, rahoton da jaridar The Punch ta fitar, ya bayyana wasu laifukan da ake zarginsa da aikatawa wadanda suka kai ga cafke shi.

A cewar rahoton, an kama Obiano ne saboda:

  1. Zargin karkatar da makudan kudade sama da N17bn na Paris Club
  2. Rashin gudanar da lamuran tsaro yadda ya kamata
  3. Bincike kan ayyukan da ake tuhuma, ciki har da aikin filin jirgin sama na Umueri wanda ake zargin an yi karin kudade a aikinsa

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Bayan hanashi guduwa Amurka, EFCC ta saki Obiano da matarsa

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, bayan damkeshi jiya da dare.

Hakazalika an saki matarsa, Ebelechukwu Obiano, bayan marin da tasha hannun Bianca Ojukwu, rahoton New Telegraph.

Har yanzu ana tattara dalilan da ya sa suka kamashi da farko.

Abin da Matar Gwamna mai barin-gado ta fada, har Bianca Ojukwu ta mare ta a taro

A wani labarin, Legit.ng ta samu karin bayani a game da abin da ya jawo rikici ya barke tsakanin Ebelechukwu Obiano da Bianca Ojukwu a ranar Alhamis.

Wadannan manyan mata biyu sun kicime da fada yayin da abin ya kai ga mari a lokacin da ake rantsar da Farfesa Charles Soludo a matsayin sabon gwamna.

Ana zargin Madam Ebelechukwu Obiano ce ta tsokano Miss Bianca Ojukwu a wajen taron bayan ta fada mata wasu kalamai da sam ba su yi mata dadin ji ba.

Kara karanta wannan

Bidiyo ya bayyana: Bianca Ojukwu ce ta kaftawa matar gwamna mai barin gado Obiano mari

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.