Ministan shari'a Malami: Ba zan yi murabus ba, sai na kammala wa'adin aiki na a mutunce
- Ministan shari’a, Abubakar Malami ya karyata rade-radin cewa ya yi murabus daga kan kujerarsa
- Malami ya bayyana cewa sai ya kai karshen wa'adin mulkinsa wanda zai kare a watan Mayun 2023
- Babban atoni janar na tarayyan ya kuma ce yana addu'an kammalawa lafiya a mutunce
Atoni janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga kujerarsa ba, inda ya bayyana cewa zai kammala wa’adin mulkinsa a mutunce a watan Mayun 2023.
Malami ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, a Abuja yayin da yake jawabi a wani taro da kungiyar masu aiko da rahotanni na shari’a ta kasa suka shirya.
Ministan ya yi watsi da rahotannin kafafen yada labarai na cewa ya yi murabus daga kujerarsa, yayin da ya bukaci manema labarai da su kasance masu gaskiya a rahotanninsu.
Ya kuma yi kira ga hukunta yan jarida da makiran yan siyasa ke amfani da su, jaridar Punch ta rahoto.
Punch ta nakalto Malami yana cewa:
“ Lokaci ya yi da yakamata mu inganta ilimin kafafen yada labarai domin yan Najeriya su ji dadin tantance gaskiyar bayanai.
“Yawancin mutane da suka dogara da wasu masu yada labarai da ba su da kwarewa za su yi mamakin ganin cewa Malami da aka ce ya yi murabus daga mukamin Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a har yanzu yana gudanar da ayyukansa da suka hada da halartar taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya a jiya, yana bayar da damar hira da manema labarai sannan kuma a yau ya bude wannan taro a matsayin Atoni Janar na tarayya.
“Akwai karshen komai. Wa’adin mulkina bai riga ya zo karshe ba. Ina addu'ar kyakkyawan karshe."
Babu ruwana: Babban sakataren gwamnatin Katsina ya karyata cewar yana da hannu a fashi da makami
A wani labarin, babban sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dr Mustapha Inuwa, ya nesanta kansa daga samun kowace alaka da yan bindiga da rashin tsaro a jihar.
Inuwa ya yi karin hasken ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a ranar Laraba, 16 ga watan Maris, a Katsina bayan ya ayyana aniyarsa ta yin takarar gwamna a zabe mai zuwa, The Nation ta rahoto.
Ya gabatar da wasika don sanar ma shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar kudirinsa.
Asali: Legit.ng