Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari
- Jajirtaccen dan sanda, Abba Kyari a yau ya cika shekaru 47 a duniya, inda aka samu akasi yana tsare a hukumar NDLEA
- A yayin da aka kama shi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya, dan sandan da aka dakatar ya kai karar hukumar ta NDLEA bisa zarginta da take hakkinsa na dan adam
- A halin yanzu dai Kyari yana tsare a hannun NDLEA bisa zargin hada wata harkalla mai karfi da safarar miyagun kwayoyi
Jajirtaccen dan sandan da aka dakatar kuma tsohon kwamandan hukumar leken asiri ta IRT, DCP Abba Kyari, wanda yanzu haka yake tsare a hannun hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ya cika shekaru 47 a duniya a yau Alhamis 17 ga watan Maris.
Abba Kyari dai a farko ya sauya tunanin 'yan Najeriya game da aikin dan sanda, inda ya zama kan gaba wajen tabbatar da kare sunan 'yan sanda saboda aiki tukuru.
To amma, lokaci daya wasu abubuwa suka faru, sai ga shi ya zama maudu'in tattaunawa a kafafen sada zumunta na kasar nan.
Kamar yadda shafinsa na Facebook ya bayyana, an haifi Kyari a ranar 17 ga Maris, 1975.
Ga abubuwan da ya kamata ku sani game da Kyari.
1. Makarantar 'yan sanda
Ya samu gurbin shiga makarantar ’yan sandan Najeriya da ke Wudil, Jihar Kano, a shekarar 2000, kuma ya kammala karatunsa a matsayin mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP).
2. Ya shiga rundunar 'yan sanda ta jihar Adamawa
An tura shi ofishin ‘yan sanda na jihar Adamawa a tsarin aikinsa na shekara guda bisa tilas, kuma ya yi aiki a sashin ‘yan sanda na garin Song.
3. Ya zama mataimakin kwamishinan 'yan sanda
Daga ASP, Kyari ya samu mukami har ya zama DCP kuma shugaban rundunar ‘yan sanda da ke ta leken asiri wato IRT da ke da hedikwata a Abuja.
An yi masa lakabi da ‘super cop’ saboda yadda ya yi amfani kwarewarsa wajen zakulo manyan masu aikata laifuka, ciki har da Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans da aka yanke masa hukunci a yanzu.
4. Sauyin rayuwa nan take
A wani al’amari mai cike da rudani, al’amura sun tabarbarewa Kyari yayin da aka alakanta shi da laifin zamba da ya kai dalar Amurka miliyan $1.1.
An zargi Kyari da wani fitaccen dan damfara, Raman Abass da aka fi sani da Hushppupi, wanda a halin yanzu yake fuskantar tuhumar karkatar da kudade a Amurka, inji rahoton Daily Trust.
Sakamakon haka aka kama shi aka tsare shi.
Baya ga haka, Abba Kyari na fuskantar shari'a tsakaninsa da hukumar NDLEA bisa zargin kulla harkallar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.
Hukumar NDLEA ta gano wasu Biliyoyin kudi kwance a cikin asusun Abba Kyari da yaronsa
A wani labarin, sababbin bayanai su na fitowa a game da tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda ta IRT, DCP Abba Kyari da kuma mataimakinsa, ACP Sunday Ubua.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa ana zargin wadannan jami’an ‘yan sanda biyu sun karbi Naira biliyan 4.2 lokacin da suke aiki kafin a ruguza tawagarsu.
Wannan yana cikin rahoton da NDLEA ta aikawa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami.
Asali: Legit.ng