2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki saboda sha'awar kujerar gwamna

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki saboda sha'awar kujerar gwamna

  • Gwamnan jihar Kaduna ya nemi ma'aikatan gwamnati da ke neman tsayawa takara da su ajiye aiki nan da karshen watan Maris
  • Gwamnan ya bayyana haka ne daidai da sabuwar dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu
  • A jihar Kaduna, an samu jami'in gwamnatin da ya nuna sha'awar kujerar El-Rufai, ana neman ya ajiye aiki

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai, ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da sauran ma’aikatan gwamnatin jihar da ke neman tsayawa takara a 2023 da su yi murabus daga ranar 31 ga Maris, 2022 ko kafin nan.

Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar, Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), wanda kuma ya rike mukamin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin El-rufai ne kadai ya ayyana aniyar tsayawa takara; yana harin kujerar El-Rufai.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai Ya Umurci Duk Masu Riƙe Da Mukaman Siyasa Da Ma'aikatan Gwamnati Masu Son Takara Su Ajiye Aiki

Dattijo zai ajiye aiki
2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa nuna sha'awar kejerar gwamna | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Dattijo ya ce idan aka zabe shi zai karfafa nasarorin da gwamnan ya samu wajen ciyar da jihar gaba, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

An kuma tattaro cewa akwai wasu masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da ke da sha’awar wani matsayi na siyasa wadanda har yanzu ba su bayyana aniyarsu ba.

A cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Jiha Balarabe Abbas Lawal ya fitar ya ce dokar zabe ta 2022 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu kwanan nan ke tafe da wannan ka'ida.

A cewar sanarwar:

“Dokar ta tanadi cewa irin wadannan jami’an su yi murabus kwanaki 30 kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar na kujerar da suke nema.
“A bisa bin wannan tanadi, duk masu rike da mukaman siyasa da sauran ma’aikatan gwamnati da ke neman mukaman siyasa a jihar Kaduna su mika takardar barin aiki ga sakataren gwamnatin jihar kafin ranar 31 ga Maris 2022."

Kara karanta wannan

Shawaran Masari ga masu rike da mukamai: Ku ajiye mukamanku kafin takara

Ku tuna cewa sashe na 84 (12) na dokar zabe da shugaban Buhari ya sanya wa hannu kwanan nan ya hana masu rike da mukaman siyasa a kasar tsayawa takara tun daga matakin fidda gwani na jam’iyya ba tare da yin murabus ba, rahoton Punch.

Na hannun daman gwamnan arewa ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga APC

A wani labarin, mai bada shawara na musamman kan harkokin gwamnati ga gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe, Alhaji Garba Jijji Gadam, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Daily Trust ta rahoto tsohon hadimin gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matakin ne bisa ra'ayin kansa, kuma ya aje mukaminsa nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Gadam ya kuma yaba wa gwamna Inuwa Yahaya bisa abin da ya kira, "babbar dama" da gawmna ya ba shi na aiki a gwamnatin jiha kuma karƙashin jagorancin shi.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.