Yan bindiga sun harbe DPO, da wasu jami'an tsaro 6 a wani kazamin hari da suka kai Neja

Yan bindiga sun harbe DPO, da wasu jami'an tsaro 6 a wani kazamin hari da suka kai Neja

  • DPOn yan sanda, jami'an yan sanda biyu da yan bijilanti hudu sun rasa rayuwarsu a kokarin daƙile harin yan bindiga
  • Kakakin yan sanda reshen jihar Neja ya bayyana cewa lamarin ya faru ranar Talata, yayin da yan ta'addan suka kai hari kauyen Nasko
  • Hukumar yan sanda ta jajanta wa mutum 7 da suka rasu sanadin harin, ta tabbatar da cewa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen magance bata gari

Niger - Aƙalla jami'an tsaro bakwai suka rasa rayukansu ciki har da shugaban ofishin yan sanda (DPO) na caji Ofis ɗin Nasko, ƙaramar hukumar Magama, jihar Neja, a harin yan bindiga ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana a yau Talata, 15 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Mafarauta a jihar Borno sun kashe katon Zaki a garin Konduga

Yan bindigan sun yi yunkurin kai hari kan jam'an ƙauyen Nasko, amma jami'an tsaro da suka haɗa da yan sanda, sojoji, da yan Bijilanti suka tarbe su.

Yan bindiga a Neja
Yan bindiga sun harbe DPO, da wasu jami'an tsaro 6 a wani kazamin hari da suka kai Neja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin yan sanda na jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce yan sanda biyu da yan Bijilanti hudu ne suka rasa rayukarsu a gwabzawar.

Punch ta rahoto Kakakin yan sanda ya ce:

"Ranar 15 ga watan Maris, 2022, ya ta'addan suka farmaki ƙauyen Nasko a karamar hukumar Magama, jihar Neja da misalin ƙarfe 1:00 na rana."
"Jami'an yan sanda da yan Bijilanti bisa jagorancin DPO na Nasko suka tarbe su, suka yi artabu har suka kashe wasu ƴan ta'addan, wasu kuma suka gudu da raunin harbi."
"Bisa rashin dace yayin musayar wuta, DPO da wasu yan sanda biyu, da yan Bijilanti huɗu suka rasa rayukansu."

Kara karanta wannan

Rikici: An kaure tsakanin sojoji da wasu matasa, an hallaka mutane akalla 6

Ya kara da cewa kwamandan rundunar soji na yankin Kontagora, ya ƙara jigbe ƙarin dakaru domin kasancewa cikin shiri kan abin da ka iya zuwa ya dawo na karya doka.

Yan sanda sun jajantawa iyalan waɗanda suka rasu

Mista Aboidun ya ce hukumar yan sanda na miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan yan sanda da yan Bijilantin da suka rasa rayuwansu a harin.

Kazalika ta tabbatar wa al'ummar jihar Neja cewa dakarunta ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen magance ayyukan ta'addanci a faɗin jihar Neja.

Legit.ng Hausa ta tuntubi wani ɗan asalin garin Nasko, Isma'il Umar, ya faɗa mana cewa DPOn da aka kashe ya jima ya na ba da shawarin yadda za'a kawo karshen ta'addancin yan bindiga.

Umar, wanda ke zaune a Minna, ya ce a makon da ya gabata yan ta'addan sun farmaki wani gidan gona a gefen garin, suka kwamushe dabbobi da dama.

Ya ce:

"Yan bindigan sun fito daga Garin Ngaski a jihar Kebbi, suka shiga wani kamfani, suka halaka yan sanda hudu da wasu mutane da dama. Daga Nagaski akwai hanyar da zata kawo ka har Nasko."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Matar Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a cikin kotu

"Sun shigo har tsakiyar gari, suka nufi Caji Ofis ɗin yan sanda na garin, suka buɗe wa jami'ai wuta har suka kashe DPO da wasu yan Banga, akalla sun halaka jami'an tsaro kusan Takwas wasu kuma sun jikkata."

Da wakilin mu ya tambaye yan bindigan sun taɓa mutanen gari, Umar ya ce:

"Gaskiya sun yi harbi, amma mutane sun gudu, sai dai waɗan da suka sami rauni. Babu sansanin sojoji kusa da garin."

A wani labarin na daban kuma mun tattaro muku Manyan kayan abinci uku da farashin su ya yi tashin gwauron zabi a kasuwar Legas a cewar yan kasuwa

Farashin kayayakin masarufi a kasuwar jihar Legas na sama suna ƙasa saboda kalubalen tsaro, canjin kudi da sauran su.

Karancin Man fetur ba ya cikin abubuwan da suka jawo tashin kayan, sai dai yan kasuwa sun ce rashin dai-daiton tattalin arziki ne babban dalili.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262