Har an fara saye: APC ta fitar da farashin sayen fom din takarar shugabancin jam'iyya
- Yayin da ake ci gaba da sa ran za a yi taron gangamin APC a cikin watan nan, jam'iyyar na ci gaba da shirye-shirye
- A yau ne jam'iyyar ta fitar jadawalin kudin sayen fom na tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar
- Jam'iyyar ta bayyana kowace da adadin kudin da za a biya domin sayen fom nan da zuwa lokacin taron gangamin
Abuja - Masu neman takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa za su biya Naira miliyan 20 kowannen su na sayen fom din tsayawa takara.
Masu neman kujerar mataimakin shugaban jam'iyya na kasa za su biya Naira miliyan 10 yayin da sauran mukamai na shugabancin za su biya Naira miliyan 5 kowanne na fom.

Source: Depositphotos
Za a gudanar da taron gangamin jam'iyyar a ranar Asabar 26 ga watan Maris.

Kara karanta wannan
2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu
The Nation ta ruwaito cewa za’a rufe siyar da fom din takarar a ranar Litinin 14 ga watan Maris.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tuni an fara sayen fom
A halin da ake ciki kuma, daya daga cikin masu neman kujerar shugaban jam'iyya na kasa kuma Turakin Ilorin, Malam Saliu Mustapha ne ya fara karbar fom din tsayawa takara tare da bayyana bukatarsa a ranar Talata, inji rahoton Vanguard.
Wasu gungun magoya bayansa da suka mamaye sakateriyar jam’iyyar ne suka karba masa fom din a madadinsa jim kadan bayan fara sayar dashi.
Siyasar Kaduna: ‘Yan gaban-goshin gwamna El-Rufai da za su kawo wanda zai gaji mulki
A wani labarin, akwai wasu ‘yan cikin gida a gwamnatin Nasir El-Rufai da ake tunanin su ne za su fito da wanda zai zama sabon gwamnan jihar Kaduna a 2023.
Wata majiya daga gidan Sir Kashim Ibrahim ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa akwai wasu mutane 11 da ke kusa da madafan ikon gwamnatin Kaduna.
Da aka yi hira da Mallam El-Rufai a gidan talabijin Channels TV a makon da ya gabata, gwamnan ya bayyana cewa yana tare da majalisar da ke zagaye da shi.
Asali: Legit.ng
