Abin Da Yasa Muka Ƙwace Filin ABU, Gwamnatin Jihar Kaduna

Abin Da Yasa Muka Ƙwace Filin ABU, Gwamnatin Jihar Kaduna

  • A ranar Litinin, gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana kwararan dalilan ta na kwace wani bangare daga cikin filin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria mai girman hekta 338
  • A cewarta, hakan ya biyo bayan sabunta takardun mallakar filin ne da jami’ar ta yi, sannan an kara karkasa filin ba bisa ka’ida ba
  • Darekta janar na hukumar tsari da bunkasa birane ta Jihar Kaduna, KASUPDA, Malam Ismail Umaru Dikko ya bayyana wa manema labarai hakan

Jihar Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana dalilinta na kwace fiye da hekta 74 a cikin filin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ABU mai girman hekta 338, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar gwamnatin, jami’ar ta sauya takardun mallakar filin ba bisa ka’ida ba, wanda ya ci karo da asalin takardun da gwamnati ta bayar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hadarin mota ya lakume mutane 11 a hanyar Zaria zuwa Kaduna

Abin Da Yasa Muka Ƙwace Filin ABU, Gwamnatin Jihar Kaduna
Dalilin Da Yasa Muka Karbe Filin ABU, Gwamnatin Jihar Kaduna. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin jihar ta ce asali tun 1965 aka bayar da takardun ga Northern Veterinary Experimental Station wacce ta koma Kwalejin kimiyar noma da kiwo ta ABU, wadanda daga bisani aka rarraba ba bisa ka’ida ba.

Sannan an sayar da hekta 81 na cikin filin zuwa filoti 900 ba bisa ka’ida ba, yayin da aka gyara filoti 426 wadanda aka yi gine-gine daban-daban.

Yayin da manema labarai suka kai ziyara filin da ake rigima akan shi wanda yake Mando, karamar hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna, Darekta Janar na hukumar tsari da bunkasa birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA), Malam Ismail Umaru Dikko, ya ce takardar mallakar dilin mai lamba 1060, ta kwalejin kimiyar noma da kiwo, wanda aka yi amfani da hekta 47 don harkokin ilimi da muhallin malamai, sai kuma wasu hekta 34.5 don noma da kiwo.

Kara karanta wannan

Kun kyauta: Amurka ta taya EFCC murnar kama mai laifin da FBI ta dade tana nema

An musanya wa jami’ar da wani fili na daban a karamar hukumar Igabi

Dikko ya ce filin ya zama barazana ga tsaron gabadaya yankin, wanda haka ya sa ya zama wajibi a kara gyara da kuma bunkasa wurin kamar yadda dokar Kaduna Master Plan ta 2016 ta tanadar.

Ya ce don gudun a ci gaba da rarraba filin ba bisa ka’ida ba, gwamnatin jihar ta yanke hekta 74 wanda zata mayar gidaje, makabartu, kasuwanni da kuma asibitoci.

Darekta Janar din na KASUPDA ya ce za a musanya wa kwalejin kimiyar noma da kowon wani fili da ke Kangimi a karamar hukumar Igabi don ta yi amfani da shi wurin kiwo.

A cewar Dikko, ABU ta yi yunkurin yin kakagida inda ta katange fiye da yawan filin da aka ba ta, ta kara yawan shi fiye da kima.

Daily Trust ta ruwaito yadda jami’ar ta zargi gwamnatin Jihar Kaduna da yunkurin kwace mata fili mai girman hekta 196.24 wanda ya ci karo da bayanin gwamnatin inda tace filin ya kai hekta 338.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164