Hush-Kyari: Ministan shari'a ya yi amai ya lashe, ya wanke Abba Kyari daga zargin damfara
- Da alama dai DCP Abba Kyari zai samu dan sararawa bayan wani martani na AGF Malami dangane da shari'ar sa ta Amurka
- Babban Lauyan na gwamnatin tarayya ya bayyana cewa babu wata shaida da ta nuna cewa babban jami’in ‘yan sandan ya saci kudi ko yana da hannu a wata damfara
- Sai dai, binciken da ‘yan sanda suka gudanar a baya ya nuna yadda ‘yan damfaran kasa da kasa karkashin jagorancin Hushpuppi suka danno N235,120,000 ga kanin Kyari
Abuja - Alamu masu karfi na nuni da cewa mai yiwuwa babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami na shirin kubutar da Abba Kyari daga fuskantar tuhuma kan zargin damfarar da ake masa a baya-bayan nan.
A karshen makon nan ne wani batu ya fito kan damfarar dala miliyan 1.1 na Hushpuppi da ta shafi Abba Kyari da sauran masu hannu a ciki, inda ofishin Malami ya fitar da wata sabuwar matsaya ta shari’a da ta wanke Kyari daga zargin hannu a damfarar.
Rahoton Punch ya ce, makwanni bayan umartar hukumar 'yan sanda ta binciki Kyari kan karbar wasu kazaman kudade, bayanan bincike sun bayyana cewa, an samu Abba Kyari da hannu dumu-dumu a wannan badakala.
Sai dai, ofishin minista malami ya fitar da sabon batu, inda yace sam babu wata hujja da ke nuna Abba Kyari yana hannu a damfarar da Hushpuppi ya yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ofishin AGF wanda a cikin batunsa na farko ya yarda cewa a farko DIG Joseph Egbunike ya jagoranci kwamitin bincike na musamman akan Kyari bisa zargin kuma ya gamsu da rahotonsu, yanzu ya ce babu wata alaka tsakanin Kyari da damfarar bayan bincike mai zurfi.
Sabuwar matsayar ta shari’a mai lamba DPPA/LA/814/21 da Mohammed Abubakar ya rubuta a madadin AGF ya jaddada cewa shaidun dake kunshe cikin littafin karar ba su nuna wata alaka tsakanin Kyari da Hushpuppi ba ta fuskar damfara, rahoton Vanguard.
Idan baku manta ba, tun farko an dakatar da Abba Kyari daga aiki saboda zargin da FBI ta kasar Amurka ta yi kan jami'in bisa hannu a wata damfarar makudan kudade.
A baya-bayan, an kuma zargi Abba Kyari da gudanar da harkallar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, wanda a halin yanzu yake fuskantar shari'a a kai.
Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis
A wani labarin, Joseph Egbunike, wanda shi ne Mataimakin Sufeta-Janar mai kula da sashen FCID na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya kwanta dama.
Rahoton da ya fito daga Punch a ranar Laraba, 9 ga watan Maris 2022 ya tabbatar da wannan labari.
Kamar yadda mu ka ji, DIG Joseph Egbunike ya fadi ne cikin ofishinsa a yammacin ranar Talata. Tun daga nan bai farfado ba, sai dai aka dauki gawarsa.
Kafin rasuwarsa, Egbunike shi ne 'dan sandan da ya jagoranci kwamitin da IGP Usman Alkali Baba ya kafa domin ya binciki abokin aikinsa, Abba Kyari.
Asali: Legit.ng