Ta hadu da bacin rana: An kama wata gurguwar karya tana bara, an tursasa ta yin tafiya a bidiyo
- Dubun wata matashiyar yarinya da ke karyar gurgunta tare da zama kan keken guragu ya cika a jihar Lagas
- Mutane sun cika da mamaki bayan da aka tilsatawa yarinyar ta tashi tsaye daga kan keken guragun kuma ya bayyana karara cewa ba gurguwa bace
- An tilasta mata yin tafiya sannan mutanen da ke wajen suka dunga tunani kan yawan kudin da ta tara a wannan harka
Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani bidiyo na wata mabaraciya da ta yi ikirarin cewa ita gurguwa ce don kawai ta tara kudi a daga harkar bara.
Yarinyar na zama ne a kan keken guragu wanda musamman ta tanade shi domin yin wannan harka da kuma yawo a yankin Ikeja tana rokon kudi daga hannun mutane a matsayin mai nakasa.
An tilasta mata yin tafiya
Lokacin da wasu matasa da suke lura da ita suka kama ta, sai suka tilasta mata sauka daga keken guragun sannan suka sa ta yin tafiya. Tana sauka, sai ya bayyana karara cewa duka kafafuwanta guda biyu lafiya suke babu abun da ya same su.
Don haka mutane da dama sun bayyana cewa bara tamkar kasuwanci ne a gare ta. Shafin @instablog9ja ya wallafa bidiyon da aka dauka na yarinyar.
Kalli bidiyon a kasa:
Mabiya shafukan zumunta sun tofa albarkacin bakunansu
@wendy_adamma ta ce:
"Irin wadannan mutanen na da yawa a nan Lagas. Kowa neman na kai yake yi dan Allah."
@michelledera ta yi martani:
"Asiri ya tonu" duk mun cika da mamaki."
@callmedamy ta yi martani:
"Kasuwa ta baci fa."
@opsyswagger ta yi martani:
"Na daina basu kudi lokacin da na gane cewa yawancinsu na amfani da dabaru iri-iri don rokon kudi."
@iambiggysteve ya yi martani:
"Wannan ta batawa ainahin guragu kasuwa."
An kama wata mabaraciya da kudi har N500,000 da dala 100 a Abuja, an tsare ta
A wani labarin kuma, mun ji cewa an kwamushe wata mabaraciya mai suna Hadiza Ibrahim a Abuja dauke da kudi N500,000 da kuma dala 100.
Jaridar Punch ta rahoto cewa mazauna yankin sun shiga rudani bayan da aka samu matar dauke da wadannan makudan kudade.
Kakakin hukumar kula da harkoki, zamantakewa da ci gaban babban birnin tarayya, Shaka Sunday, ya tabbatar da cewar matar na tsare a hannun hukumar a yankin Bwari.
Asali: Legit.ng