Jihar Bauchi ta ware miliyan N100 don karatun Al-Qur’ani

Jihar Bauchi ta ware miliyan N100 don karatun Al-Qur’ani

  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya amince da naira miliyan 100 domin gudanar da gasar karatun Al-Qur'ani na 2022 a jihar
  • Wannan shine karo na uku da jihar Bauchi ke za ta karbi nauyin shirya gasar na kasa tun bayan fara ta a 1986
  • Gwamnan ya ce kwamitin gasar ya gabatar masa da naira miliyan 153 amma gwamnatin za ta bayar da miliyan 100 sai a nemi sauran a wani wurin

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da naira miliyan 100 domin gudanar da gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 36 na shekarar 2022 a jihar.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan a yayin bikin rantsar da mambobi 57 na kwamitin shirya gasar a ranar Asabar, 12 ga watan Maris, a garin Bauchi, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda Mai Mala Buni da shugabannin APC suke fama da shari’a fiye da 200 a gaban kotu

Jihar Bauchi ta ware miliyan N100 don karatun Al-Qur’ani
Gwamnatin Bauchi ta ware miliyan N100 saboda gasar Al-Qur’ani
Source: UGC

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rahoto cewa an shirya gudanar da gasar ta kasa a Bauchi daga ranar 18-20 ga watan Maris.

Mohammed ya ce wannan ne karo na uku da jihar Bauchi za ta karbi nauyin gasar tun bayan fara ta a 1986.

Ya ce:

“Ina son bayyana cewa ma’aikatar harkokin addini, tare da hadin gwiwar jami’ar Usman Dan Fodio ta Sokoto da sauran hukumomin gwamnati sun gabatar da kasafin kudi na naira miliyan 153 na gasar.
“Gwamnatin jihar za ta samar da naira miliyan 100 ga wannan kwamitin domin a samo sauran a wani wurin.”

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani

A wani labari, Babban malamin darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana sirrinsa na haddar Al-Qur'ani mai girma.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Kamar yadda malamin ya sanar da BBC Hausa a wata tattaunawa da tayi da shi, ya ce suna da wani sirri da iyayensu suka samo na hadda daga Borno wajen kabilar Bare-Bari.

"Daga baya yayin da Sheikh Ibrahim Inyass ya bayyana, ya roki Allah da ya bada karamar haddar Alkur'ani. Hakan ne yasa aka huta nemo maganin karatun Alkur'ani. Shehu ne ya riga ya rokawa mutane kuma ake hadda cikin sauki," a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng