Mun cire tallafin lantarki a boye gaba daya, zamu cire na man fetur: Gwamnati ga IMF
- Gwamnatin tarayya ta bayyanawa asusun lamunin duniya cewa ta cire tallafin wutan lantarki gaba daya ta hanyar kara farashin wuta kadan-kadan
- Ministar ta ce da sannu gwamnatin tarayya zata cire na man fetur duk da hayaniyan da ake yi
- A cewarta, a shekarar nan suka yi niyyar cire tallafin amma yan Najeriya suka ki yarda
Ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta cire tallafin wutan lantarki gaba daya a boye, kuma tana shirin cire na man fetur.
Hajiya Zainab, ta bayyana hakan ne a taron asusun lamunin duniya (IMF) da ya gudana ta yanar gizo, rahoton Vanguard.
Ta ce karin farashin danyen mai a kasuwar duniya na kara yawan kudin tallafin da gwamnatin tarayya ke biya.
Zanaib tace sun fara cire tallafin da gwamnati ke badawa amma,
"Mun samu koma baya ne, A Yulin shekarar nan ya kamata mu cire na mai amma jama'a suka yi ca."
"Zabe na zuwa da kuma wahalar da mutane da kamfanoni suka sha sakamakon annobar COVID-19, sai muka canza shawara."
"Amma a boye mun cire tallafin lantarki gaba daya, yanzu ko sisi basu biya kudin tallafi wuta. Mun yi haka ne kadan-kadan ta hanyar kara kudin lantarki."
"Tallafin mai babban matsala ne garemu. Yanzu dai muna gyara kasafin kudi. Muna kyautata zaton cewa yan majalisa zasu yarda don mu cigaba da shirin cire na mai, idan ba haka ba yadda abubuwa ke gudana bamu san yadda zata kasance ba"
Tsadar man fetur: Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari
Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur ya bayyana cewa yanzu haka Najeriya na da lita biliyan 1.9 na man fetur a ajiye.
A cewarsa, wannan mai na iya gamsar da bukatun kasar na tsawon kwanaki 32
Ministan ya bayyana haka ne jiya Laraba 9 ga watan Maris a Abuja yayin da yake magana a gaban majalisar zartarwa ta tarayya a zaman da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Babban Manajin Darakta na Kamfanin Mai na Najeriya Mista Mele Kyari ya raka shi a taron na FEC da aka yi.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande ne ya bayyana haka bayan taron.
Asali: Legit.ng