Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Yi Ƙarin Haske Kan Jitar-Jitar Cewa Ya Shiga Hannun Ƴan Bindiga
- Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Col. Samaila Yombe mai murabus ya musanta batun cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi wanda aka dinga yadawa
- Ya musanta batun ne a ranar Alhamis bayan yaduwar labari akan yadda ‘yan bindiga suka kai wa tawagarsa farmaki a can kudancin jihar
- Ya yi wannan bayanin ne ga manema labarai a Birnin Kebbi inda yace mugun wasa ne ace ‘yan bindiga su rike shi, ya ce ko makamancin hakan bai faru ba
Kebbi - Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Col. Samaila Yombe, mai murabus a ranar Alhamis ya musanta batun labaran da ake ta yada wa kan cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi yayin da suka kai wa tawagarsa farmaki bayan ya kai wa sojoji ziyara a kudancin jihar.
Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da wakilin Daily Trust a Birnin Kebbi.
Yana sahun gaba a ziyarar da ya kai wa rundunar sojin wacce ya kira da ‘Ziyarar filin dagar Sojoji’ don samun damar gane shiri da salon da sojojin suke amfani da shi wurin yakar ‘yan bindiga.
Ya ce ko kusa da garkuwa da shi basu yi ba
Col. Yombe ya ci gaba da bayani akan yadda ya raka kwamandan sojin a sahun gaba don ganin yadda suke aiwatar da ayyukansu.
Ya ci gaba da bayyana yadda ‘yan bindigan suka cakuda da mutanen kauyen Kanya inda suka kai wa sojojin farmaki hakan ya janyo musayar wuta a wajen kauyen.
Mutane da dama sun cutu yayin fadan sakamakon musayar wutar da suka yi. Amma Yombe ya ce ba zai sanar da yawan su ba.
A cewarsa sai bayan sun fita daga kauyen ne suka fara batakashi
Ya kada baki ya ce:
“Mugun wasa ne wannan, ga ‘dan bindiga ya rike ni a hannun sa, wannan ko a mafarki ban gan shi ba. Ko makamancin hakan bai faru ba.
“Kana ganin yadda nake zaune yanzu haka a cikin gida na cikin sakewa da walwala tamkar tsuntsun da aka saki ace ina hannun ‘yan bindiga.
“Rundunar soji daga Bataliyar Zuru ta Tank 232 wacce ta kunshi sojoji 30 zuwa 35 ne ta raka kwamandan sojin, daga nan na shiga cikin su da shirin kai wa sojin ziyara.”
Ya ci gaba da bayyana yadda mazauna kauyen Kanya suka cakuda da ‘yan bindigan, wanda hakan ya janyo sojojin suka kasa bude musu wuta don gudun taba mai uwa da wabi.
Sai dai a cewarsa, yayin da rundunar sojin ta bar kauyen, ‘yan bindigan sun biyo su, daga nan ne aka fara batakashi.
Kamar yadda ya ce:
“Bayan sun biyo sojojin wajen kauyen ne aka yi musayar wuta. Amma ba zan iya sanar da yawan wadanda lamarin ya shafa ba.”
Asali: Legit.ng